Gwamnan APC Ya Gana da Tsohon Shugaban Ƙasa, Ya Fadi Yadda Zasu Lallasa Atiku a Arewa

Gwamnan APC Ya Gana da Tsohon Shugaban Ƙasa, Ya Fadi Yadda Zasu Lallasa Atiku a Arewa

  • Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, yace Atiku zai sha ƙasa a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya
  • Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, ya fito daga jihar Adamawa, ɗaya daga jihohin shiyyar
  • Gwamnan ya ziyarci tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Albdulsalami Abubakar, domin gaida shi bayan fama a Landan

Minna, Niger - Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa ɗan takarar shugaban kasa a inuwar PDP ba zai kai labari ba a shiyyar arewa maso gabas.

"Mu ke da damar samun nasara kuma muna da karfin ɗaura ɗamarar aiki tukuru domin ganin jam'iyyarmu ta samu galaba a zaɓe," inji shi kamar yadda Punch ta ruwaito.

Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe.
Gwamnan APC Ya Gana da Tsohon Shugaban Ƙasa, Ya Fadi Yadda Zasu Lallasa Atiku a Arewa Hoto: Inuwa Yahaya/facebook
Asali: Facebook

Gwamna Yahaya ya yi wannan furucin ne a Minna, babban birnin jihar Neja yayin da ya kai ziyara ga tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Abdulsalami Abubakar, ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Bayan Tinubu, Wani Gwamnan APC Ya Faɗi Wanda Yake Kaunar Ya Gaji Buhari a 2023

Da 'yan jarida suka tambaye shi kan ɗan takarar da zai mara wa baya, Asiwaju Bola Tinubu, na jam'iyyarsa ta APC ko Atiku Abubakar, da yake ɗan uwansa, gwamnan yace ba zancen ɗan jam'iyya ko ɗan uwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yahaya ya ƙara da cewa Najeriya ƙasa ɗaya ce dunƙulalliya kuma ta fi ƙarfin ɗaukar ɓangare guda. A kalamansa, gwamnan yace:

"Ba ruwana dan yankin mu ɗaya da Atiku, dukkan su 'yan uwana ne, Najeriya ƙasa ɗaya ce, kokarin mu ta cigaba da zama ƙasa dunƙulalliya da ba zata rabu ba."

Meyasa ya ziyarci Abdulsalami?

Gwamnan ya bayyana cewa ya dira Minna ne domin ya ziyarci Abdulsalami kan rashin lafiyar da ya yi har aka kwantar da shi a Asibitin Landan.

"Mun zo mu masa fatan Alheri da samun sauki cikin hanzari. Ya kasance Uba a gare mu kuma Dattijon ƙasa, sannan mutum da ake ganin girmansa, bisa haka muka zo domin nuna kulawarmu a kansa."

Kara karanta wannan

2023: Hanya Ɗaya Da Zamu Kawo Karshen Rikicin Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar Ya Magantu

Dalilin da yasa muke zaune lafiya a Gombe - Inuwa

Gwamna Yahaya yace jihar Gombe na zaune lafiya duk da halin da ake ciki ne saboda sun gano saɓanin dake tsakanin mutane kuma sun ɗauki mataki.

A wani labarin kuma Atiku Ya Goyi Bayan Babbar Bukatar Gwamna Wike, Sabbin Bayanan Sulhun PDP Sun Fito

Jigon jam'iyyar PDP yace a halin da ake ciki Atiku ya amince shugaban jam'iyya na ƙasa ya sauka daga kujerarsa.

Katch Ononuju, yace ya kamata Atiku ya tabbatar da ikirarinsa na mai haɗa kai ta hanyar daidaita PDP ta zauna daram cikin zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262