Fitaccen Gwamnan APC Ya Kara Nada Sabbin Hadamai 86 A Jiharsa Daf Da Karewar Wa'adinsa
- Farfesa Ben Ayade, gwamnan Jihar Rivers ya nada sabbin hadimai guda 86 a hukumomi da kwamitoci daban-daban a jiharsa
- Mista Linus Obogo, sakataren watsa labarai na gwamna Ayade ne ya sanar da nadin da ya ce za su fara aiki nan take
- A baya, Ayade ya nada masu bada shawarwari da hadimai 190 duk dai a tsarin gwamnatinsa na 'tabbatar da kowa ya ci abinci'
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Cross Rivers - Gwamnan Jihar Cross Rivers, Farfesa Ben Ayade ya kara nada mutum 86 a hukumomi daban-daban da kwamitoci a yayin da mukinsa ke zuwa karshe a 2023.
A cewar sanarwar da mataimakin sakataren watsa labaran gwamnan, Linus Obogo, ya fitar, ya ce nadin za su fara aiki nan take.
Mafi yawancin wadanda aka yi wa nadin za su yi aiki a kwamitin hada kan al'umma, The Punch ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sauran da aka nada za su yi aiki a kwamitin kula da kadarorin gwamnati da kuma direktocin hukumomi da mambobin wasu kwamitocin.
Gwamnan, ta tsarinsa na 'Samar da abinci' ga mutane, ya nada hadimai da yawa a wa'adinsa na farko da biyu a ofis.
Gwamna Ayade ya nada sabbin hadimai 190
Tunda farko, kun ji cewa Gwamna Ayade ya amince da nadin sabbin hadimai da suka hada da masu taimaka masa da mashawarta na musamman.
Mashawarcin gwamnan na musamman a kan kafafen watsa labarai, Christian Ita ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
A cewar Ita, gwamnan ya yi sabbin nadin ne bisa tsarin gwamnatinsa na 'tabbatar da kowa ya ci abinci.'
Asali: Legit.ng