Gwamna Ayade ya nada sabbin hadimai 190

Gwamna Ayade ya nada sabbin hadimai 190

Gwamna jihar Cross River Ben Ayade ya amince da nadin sabbin hadimai da suka hada da masu taimaka masa da mashawarta na musamman.

Mashawarcin gwamnan na musamman a kan kafafen watsa labarai, Christian Ita ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

A cewar Ita, gwamnan ya yi sabbin nadin ne bisa tsarin gwamnatinsa na 'tabbatar da kowa ya ci abinci.'

Gwamna Ayade ya nada sabbin hadimai 190
Gwamna Ayade ya nada sabbin hadimai 190. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

Wasu daga cikin wadanda aka nada sun hada da;

1. Musa Adede – Shugaban asusun tsaro

2. Bai Thompson – Mashawarci na musamman kan masu saka hannun jari na kasa da kasa

3. Aboh Akongfe – Mataimaki na musamman kan sufirin jiragen sama

4. Anthony Bassey – Mataimaki na musamman kan harkokin 'yan gudun hijira

5. Edict Essun – Mamba, Cibiyar kare hakkin masu talla

6. Michael Ogbeche – Mamba, Kwamitin daidaito

DUBA WANNAN: Mataimakin shugaban APC ya yi watsi da sabuwar umurnin kotu

7. Joshua Ani-Ita – Mataimaki na musamman kan harkokin tarbar baki

8. Alice Achi – Babban mataimaki na musamman kan harkokin cigaban mata

9. Ekpo Ekpenyong – Babban mataimaki na musamman kan inganta wuraren shakawata

10. Dan Unah – Mataimaki na musamman kan samar da ayyuka

11. John Abese – Mamba a Hukumar kula da masu zuwa ci rani

12. Vincent Egbe – Mamba a hukumar 'yan gwan-gwan da kuma wasu saura.

A ranar 21 ga watan Afrilun 2020, Gwamna Ayade ya amince da nadin wasu hadimai 427 kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Christian Ita, hadimin gwamnan kan kafafen watsa labarai ya sanar da hakan.

Ya ce wadanda aka nada sun hada da ciyomomin hukumomi, mambobin kwamiti da masu taimaka masa na musamman.

Daya daga cikinsu har da mataimaki na musamman a kan kamfanonin samar da man gyada.

A watan Janairun 2020, gwamnan ya amince da nadin wasu hadiman 90, hakan ya kawo jumullan hadimansa zuwa a kalla 517.

Da majiyar Legit.ng ta tuntubi kakakin gwamnan, Ita ya ce gwamnan ya yi nadin ne domin rage wa mutane radadin rayuwa sakamakon annobar coronavirus.

Ya ce anyi nadin ne domin mutane su samu ayyukan yi.

Ya ce an nada mataimakin na musamman a kan kamfanonin samar da man gyda ne saboda sabbin masana'antar samar da man gyada da ake ginawa a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164