NNPP Ta Garzaya Kotu, Tana Son A Haramta Wa Dukkan Yan Takarar APC Na Kaduna Shiga Zaben 2023

NNPP Ta Garzaya Kotu, Tana Son A Haramta Wa Dukkan Yan Takarar APC Na Kaduna Shiga Zaben 2023

  • Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, ta shigar a kara a babban kotun tarayya na Kaduna tana neman a haramtawa yan takarar APC shiga zaben 2023
  • Jam'iyyar mai alaman kayan marmari ta shaidawa kotun cewa yan takarar na APC ba su bi ka'idojin zaben fidda gwani ba don haka bai cancanta su shiga zaben ba
  • A baya-bayan nan, wasu kungiyoyin matasa na jam'iyyar NNPP sun bukaci jam'iyyar ta canja dan takarar gwamnanta, Suleiman Hunkuyi kan zarginsa da cin amanar jam'iyya

Jihar Kaduna - Jam'iyyar NNPP ta garazaya babban kotun tarayya da ke Kaduna tana kallubalantar halascin yan takarar jam'iyyar APC a jihar, The Cable ta rahoto.

A karar da ke gaban Mai shari'a, Hadiza Shagari, NNPP tana neman kotun ta haramtawa dan takarar gwamna na APC a Kaduna da yan majalisun jihar shiga zaben 2023.

Kara karanta wannan

Zaben Ekiti da Osun: INEC ta ce wasu madatsa sun farmaki tashar yanar gizonta

Yan APC
Kaduna: NNPP Ta Bukaci Kotu Ta Haramta Wa Dukkan Yan Takarar APC Shiga Zabe. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

Yan takarar APC ba su ci zabe ta halastaciyar hanya ba - NNPP

NNPP ta yi ikirarin cewa yan takarar da sunayensu ke jerin sunan da INEC ta wallafa ba su ci zabensu da hanyar da doka ta tanada ba a Electoral Act, 2022 da wasu dokokin yin zaben fidda gwani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Don haka, jam'iyyar tana rokon kotun ta umurci INEC 'ta dauki matakin da ya dace na cire sunayen yan takarar daga jerin yan takarar da suka cancanci yin takara a babban zaben jihar Kaduna a 2023'.

A cewar NAN, shari'ar da aka ambata a ranar Juma'a, an dage cigaba da sauraronsa zuwa ranar 15 ga watan Satumba.

Alkaliyar ta yi bayanin cewa an dage cigaba da sauraron karar ne saboda ba a riga an bawa jam'iyyun da abin ya shafa takardun da INEC ta bawa kotun ba.

Kara karanta wannan

Jam'iyya Ta 'Kori' Shahararren Dan Takarar Shugaban Kasarta Gabanin Zaben Shekarar 2023

Alkalan NNPP da APC sun yi martani

Wole Agunbiade, shugaban lauyoyin NNPP, ya shaidawa kotu cewa INEC ba ta riga ta bashi takardar kara ba.

A bangarensa, Sule Shuaibu, shugaban lauyoyin APC ya ce an bashi takardar amma yana bukatar lokaci ya yi nazari kafin ya taho ya kare kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164