2023: Yadda Zamu Kawo Karshen Rikicin Jam'iyyar PDP, Atiku Ya Magantu

2023: Yadda Zamu Kawo Karshen Rikicin Jam'iyyar PDP, Atiku Ya Magantu

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce zasu bi hanya ɗaya domin warware rikicin da ya addabi jam'iyyar PDP
  • Ɗan takarar ya kuma sha alwashin cewa zai baiwa mara ɗa kunya idan har ya zama shugaban Najeriya a zaben 2023
  • Wannan ne zuwa yayin da NEC ta kaɗa kuri'ar amincewa da Ayu a matsayin shugaban PDP na ƙasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sha alwashin cewa zai baiwa maraɗa kunya idan aka zaɓe shi shugaban ƙasan Najeriya a 2023.

Premium Times ta ruwaito cewa Atiku ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi a taron majalisar zartarsa (NEC) karo na 97 a birnin tarayya Abuja ranar Alhamis.

Atiku Abubakar.
2023: Yadda Zamu Kawo Karshen Rikicin Jam'iyyar PDP, Atiku Ya Magantu Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya kuma yaba wa mambobin NEC bisa namijim kokari da goyon bayansu yayin babban taro na musamman wanda ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a watan Mayu.

Kara karanta wannan

"Dole Ya Sauka" Gwamna Wike Ya Maida Zazzafan Martani Ga Majalisar Koli Ta PDP Kan Ayu

"Ba zan iya gode muku yadda ya kamata ba, alƙawarin da zan ɗaukar muku shi ne zan ba maraɗa kunya game da tsammanin da kuke mun da burin yan Najeriya a kaina."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Bari na yi amfani da wannan damar na kara gode wa shugaban BoT mai barin gado bisa sadaukarwarsa da fifikon da ya nuna wa jam'iyyar mu."

- Atiku Abubakar.

Yadda zamu magance rikicin cikin gida a PDP - Atiku

A ruwayar Punch, Tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya bayyana shirinsa na warware duk wasu ƙulli da suka hana jam'iyyar PDP zaman lafiya a cikin gida.

"Masu magana sun yi tsokaci kan rikicin iyali ɗaya, saɓanin iyali abu ne da ya saba faruwa ko Iyalai na jini ɗaya haka zalika iyalin da siyasa ta haɗa su."
"Amma ina mai baku tabbacin cewa mun shirya warware matsalolin nan a cikin gida, babu wata matsala muhimmiya, abu ne da ya saba faruwa."

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Goyi Bayan Babbar Bukatar Gwamna Wike, Sabbin Bayanan Sulhun PDP Sun Fito

Bugu da ƙari, Atiku ya yi kira ga mambobi su tabbatar babu wata hanya da suka bi face ta cikin gida wajen warware rikicin kana su kiyaye tanade-tanaden kundin dokokin jam'iyya.

A wani labarin kuma An Naɗa Sabon Shugaban BoT Na Ƙasa Bayan Walid Jibrin Ya Yi Murabus Yau a Abuja

Shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP ta ƙasa (BoT), Sanata Walid Jibrin, ya sauka daga kan muƙaminsa.

Bayanai sun nuna cewa an naɗa Sanata Adolphus Wabara, tsohon shugaban majalisar Dattawa a matsayin muƙaddashin shugaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262