2023: Atiku Na Bukatar Shugaban Jam'iyya Ya Yi Murabus, Jigon PDP

2023: Atiku Na Bukatar Shugaban Jam'iyya Ya Yi Murabus, Jigon PDP

  • Jigon jam'iyyar PDP yace a halin da ake ciki Atiku ya amince shugaban jam'iyya na ƙasa ya sauka daga kujerarsa
  • Katch Ononuju, yace ya kamata Atiku ya tabbatar da ikirarinsa na mai haɗa kai ta hanyar daidaita PDP ta zauna daram cikin zaman lafiya
  • An nemi zaman lafiya an rasa a jam'iyyar PDP tun bayan gama zaɓen fidda gwani da zaɓen abokin takarar Atiku

Abuja - Jigon jam'iyyar PDP, Katch Ononuju, ya yi ikirarin cewa ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, yana son shugaban jam'iyyya na kasa, Iyorchia Ayu, ya sauka daga kujerarsa.

Mista Ononuju ya yi wannan furucin ne yayin da yake hira a kafar Talabijin Channels tv a shirin Sunrise Daily ranar Alhamis, yayin da yake tsokaci kan rikicin PDP.

Kara karanta wannan

Tsoho Ministan Ya Fallasa Wani Sirri, Ya Faɗi Abu Ɗaya Da Zai Sa Yan Najeriya Su Zaɓi APC a 2023

Rikicin jam'iyyar PDP.
2023: Atiku Na Bukatar Shugaban Jam'iyya Ya Yi Murabus, Jigon PDP Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Haka nan jigon PDP ya yi karin haske kan batun saɓanin ɗake tsakanin Gwamnan Ribas, Nyesom Wike da Atiku, inda yace ba Wike kaɗai ke son Ayu ya sauka ba.

Jaridar Punch ta ruwaito Ononuju na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A bayanan da na samu, ɗan takara (Atiku) yana son Ayu ya yi murabus, amma akwai 'yan hana ruwa gudu a jam'iyya, wadan ke zuga Ayu, suna faɗa masa kar ya sauka, ban san dalilin su ba."
"Ɗan takarar shugaban ƙasa yana son Ayu ya yi murabus matuƙar hakan zai kawo zaman lafiya a cikin gida domin tunkarar zaɓe. Idan Atiku zai cigaba da ikirarin shi mai haɗa kai ne, to ya kamata mugani a ƙasa a jam'iyya."

Abinda ya kamata Atiku ya aikata - Katch Ononuju

Bugu da ƙari, Jigon PDP yace ba wai a fatar baki kawai ya kamata Atiku ya faɗa ba, ya aikata a zahirance wajen daidaita jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku Abubakar da Gwamna Wike Sun Amince da Bukata Ɗaya Kafin Fara Kamfen 2023

"Ba ya bukatar ya nuna so kaɗai, ya kamata ya aikata a zahirance game da batun daidaita jam'iyya ta hanyar haɗa kai da wasu wajen tabbatar da Ayu ya sauka daga shugabanci domin jam'iyya ta zauna dai-dai."

Ononuju, ya ƙara da cewa fafutukar maye gurbin Ayu da wani ɗan kudu ya zarce Wike kaɗai, bukata ce da dukkanin jiga-jigan PDP daga Kudu, waɗanda ba su son ganin yan arewa sun mamaye muƙamai uku.

A wani labarin kuma kun ji cewa shugaban BoT-PDP na ƙasa, Sanata Walid Jibrin, ya sauka daga kujerarsa kuma tuni aka naɗa sabon shugaba

Shugaban kwamitin amintattu (BoT) na jam'iyyar PDP ta ƙasa, Walid Jibrin, ya yi murabus daga mukaminsa.

A wani rahoto da jaridar Vanguard ta ci karo da shi, tuni aka ayyana tsohon shugaban majalisar Dattawa, Adolphus Wabara (Daga yankin kudu maso Gabas), a matsayin muƙaddashin shugaban BoT.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262