Shugaban BoT Na Jam'iyyar PDP Ta Ƙasa, Walid Jibrin, Ya Yi Murabus Daga Kujerarsa

Shugaban BoT Na Jam'iyyar PDP Ta Ƙasa, Walid Jibrin, Ya Yi Murabus Daga Kujerarsa

  • Shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP ta ƙasa (BoT), Sanata Walid Jibrin, ya sauka daga kan muƙaminsa
  • Bayanai sun nuna cewa an naɗa Sanata Adolphus Wabara, tsohon shugaban majalisar Dattawa a matsayin muƙaddashin shugaba
  • Wannan sauyi na zuwa a lokacin da ake ta kiraye-kirayen shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya fice daga Ofis

Abuja - Shugaban kwamitin amintattu (BoT) na jam'iyyar PDP ta ƙasa, Walid Jibrin, ya yi murabus daga mukaminsa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Jibrin ya sanar da matakin ne a taron majalisar zartarwar PDP (NEC) wanda yanzu haka yake ci gaba da gudana a Abuja.

Sanata Walid Jibrin.
Shugaban BoT Na Jam'iyyar PDP Ta Ƙasa, Walid Jibrin, Ya Yi Murabus Daga Kujerarsa Hoto: channelstv
Asali: Facebook

A wani rahoto da jaridar Vanguard ta ci karo da shi, tuni aka ayyana tsohon shugaban majalisar Dattawa, Adolphus Wabara (Daga yankin kudu maso Gabas), a matsayin muƙaddashin shugaban BoT.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Goyi Bayan Babbar Bukatar Gwamna Wike, Sabbin Bayanan Sulhun PDP Sun Fito

Tsohon shugaban wanda saura yan watanni wa'adinsa ya kare, ya yi korafin cewa an fifita wani yanki a manyan kujerun jam'iyya biyo bayan nasarar Atiku Abubakar ta zama ɗan takarar shugaban ƙasa, kuma ɗan arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ya yanke sauka daga muƙamin?

Jibrin yace, "Na ɗauki wannan matakin ne duba da kalaman da na yi a baya. Na faɗi cewa muna son mu tabbatar Atiku ya zama shugaban ƙasa ta kowane hali kuma maganar gaskiya haka ne ya sa na yanke barin BoT."

"Mun tattauna wannan batun da ɗan takarar shugaban kasa kuma ya amince da ni. Ina da yaƙinin cewa idan jam'iyyar mu ta kai ga nasara, za'a bani babbar kujera."

Wabara ya maye gurbin Jibrin

Bayan murbus din Jibirin, an amince tsohon shugaban majalisar Dattawa, Adolphus Wabara, ya zama muƙadsashin shugaban BoT na ƙasa.

Kara karanta wannan

Gwajin DNA: Bayan Shekaru 20 Da Aure, Liktita Ya fadawa Magidanci Dukkan 'Yayan Matarsa 5 Ba Nasa Bane

Wabara, wanda kafin wannan lokaci, shi ne Sakataren BoT na ƙasa, yana daga cikin waɗan da zasu shiga tawagar yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa.

A wani labarin kuma Shugabannin APC da Dumbin Magoya Baya Sun Sauya Sheka Zuwa PDP A Sakkwato

Sakataren APC da mataimakin Ma'ajiyi a wata Gundumar jihar Sakkwato sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP

Jami'in hulɗa da jama'a na PDP, Sahabi Sanyinnawal, yace bayan haka akwai wasu jiga-jigan APC da dandazon magoya baya da suka bi sahunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262