Jerin Sunaye: Gwamnan Jihar Gombe Ya Nada Sabbin Manyan Hadimai

Jerin Sunaye: Gwamnan Jihar Gombe Ya Nada Sabbin Manyan Hadimai

  • Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya naɗa sabbin mashawarta na musamman da manyan masu taimaka masa
  • A wata sanarwa da kakakin gidan gwamnati, Mr Ismail Misili, ya fitar ya bayyana sunayen mutanen da gwamna ya naɗa da muƙamansu
  • Gwamna Yahaya na jam'iyyar APC ya yi wannan naɗin ne yayin da ya rage ƙasa da watanni Shida gabanin babban zaɓen 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Gombe - Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya naɗa sabbin mashawarta na musamman hudu da kuma manyan masu taimaka masa guda uku, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Wannan na kunshe a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Darakta Janar na ofishin yaɗa labaran gidan gwamnatin Gombe, Mr Ismail Misili, wacce aka fitar ranar Laraba.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe.
Jerin Sunaye: Gwamnan Jihar Gombe Ya Nada Sabbin Manyan Hadimai Hoto: Inuwa Yahaya
Asali: UGC

Misili ya ƙara da cewa naɗin mutanen ya fito ne daga ofishin Sakataren Gwamnatin Gombe, Ibrahim Njodi, kuma zasu fara aiki nan take ba tare da ɓata lokaci ba.

Kara karanta wannan

Bayan Shan Kaye, Gwamnan APC Ya Amince da Ɗaukar Sabbin Ma'aikata, Lamarin Ya Tada Ƙura

Jerin sunayen mutanen da gwamna ya naɗa

Ya ƙara da cewa mashawarta na musamman da aka naɗa sun haɗa da, Shuaibu Gara-Gombe (Labarai da dabaru), Shuaibu Kashere, (harkokin ma'aikata), Abdulkadir Malle, (Alaƙar gwamnatoci), da Bello Suleiman (harkokin majalisa).

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai kuma manyan masu taimaka wa na musamman wanda suka ƙunshi, Baba Mato -Kumo a matsayin SSA I kan harkokin kasuwancin yankuna, Dahiru Mohammed a matsayin SSA II kan harkokin siyasa.

Sanarwan ta kara da cewa gwamnan ya naɗa Habu Kalshingi, a matsayin babban mai taimaka masa ta ɓangaren harkokin siyasa (SSA II), kamar yadda hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta ruwaito.

A wani labarin kuma Atiku Abubakar Zai Gana da 'Yan Takarar Shugaban Kasa Da Ya Gwabza da Su a Zaben Fidda Gwanin PDP a Abuja

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, zai gana da ƴan takarar da suka fafata a zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP yau.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Buhari Tace Ta Magance Mafi Munin Matsalar Tsaro a Najeriya

Wannan taron zai gudana ne ƙasa da awanni 24 bayan Atiku ya tattauna da tsofaffin mambobin majalisar wakilai na PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262