Lamiɗo, da Wasu 'Yan Takarar Gwamna 16 a Inuwar PDP Sun Shiga Ganawa da Wike

Lamiɗo, da Wasu 'Yan Takarar Gwamna 16 a Inuwar PDP Sun Shiga Ganawa da Wike

  • Yan takarar gwamna a jihohin Najeriya akalla 17 a inuwar PDP sun Dira Patakwal, sun shiga ganawa da Wike
  • Wata majiya ta tabbatar da cewa an fara taron kofa kulle da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Talata 6 ga watan Satumba, 2022
  • Ana kyautata zaton sun je rarrashin gwamna Nyesom Wike na Ribas ne kan rikicin dake tsakaninsa da Atiku

Rivers - Ɗan takarar gwamnan jihar Jigawa karkashin inuwar PDP, Mustapha Sule Lamido, da wasu takwarorinsa daga jihohi 16 sun ziyarci gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a gidansa na kai da kai dake Patakwal ranar Talata.

Jaridar Leadership ta tattaro cewa masu neman kujerar gwamna a inuwar PDP da suka ziyarci Wike sun haɗa da na jihar Kaduna, Isa Ashiru Kudan, da na jihar Katsina, Yakubu Lado Ɗanmarke da sauran su.

Kara karanta wannan

2023: Daga Karshe, An Warware Saɓanin Dake Tsakanin Atiku da Wike, Ɗan Takarar PDP Ya Faɗi Abinda Ya Rage

Yan takarar gwamna a PDP.
Lamiɗo, da Wasu 'Yan Takarar Gwamna 16 a Inuwar PDP Sun Shiga Ganawa da Wike Hoto: Port Harcourt Political Affairs/Facebook
Asali: Facebook

Bayanai sun nuna cewa yan takarar sun dira Patakwal, babban birnin jihar Ribas da misalin ƙarfe 8:00 biyo bayan rikicin da ya ƙi ci kuma ya ƙi cinyewa a PDP yayin da ake tunakar 2023.

Ana kyautata zaton cewa sun je ne domin su rarrashi gwamna Wike ya yafe wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu da sauran shugabannin da suka ɓata masa rai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit.ng Hausa ta gano cewa a halin yanzun da muke kawo muku wannan rahoton yan takarar na can sun keɓe da Wike suna tattauna wa.

Sai dai babu tabbacin cewa ko tura su a kai su rarrashi gwamnan Ribas ko kuma sun je ne bisa ra'ayin kansu da ganin ya dace, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Wata Majiya mai kwarin guiwa ta tabbatar da wannan cigaban, inda ta bayyana cewa taron ya fara da misalin ƙarfe 8:00 na daren Talata, 6 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku Abubakar da Gwamna Wike Sun Amince da Bukata Ɗaya Kafin Fara Kamfen 2023

Hotunan yan takarar PDP

Yan takarar PDP a Patakwal.
Lamiɗo, da Wasu 'Yan Takarar Gwamna 16 a Inuwar PDP Sun Shiga Ganawa da Wike Hoto: Port Harcourt Political Affairs/Facebook
Asali: Facebook

Yan takarar gwamna a PDP.
Lamiɗo, da Wasu 'Yan Takarar Gwamna 16 a Inuwar PDP Sun Shiga Ganawa da Wike Hoto: Port Harcourt Political Affairs/Facebook
Asali: Facebook

Yan takarar gwamna a PDP.
Lamiɗo, da Wasu 'Yan Takarar Gwamna 16 a Inuwar PDP Sun Shiga Ganawa da Wike Hoto: Port Harcourt Political Affairs/Facebook
Asali: Facebook

A wani labarin kuma Tsoho Ministan Ya Fallasa Wani Sirri, Ya Faɗi Abu Ɗaya Da Zai Sa Yan Najeriya Su Zaɓi APC a 2023

Tsohon ministan wasanni a Najeriya kuma ɗan takarar Sanatan Kwara ta tsakiya yace ba ɗan Najeriyan da zai zaɓi APC a 2023.

Mallam Bolaji Abdullahi, mai neman sanata a inuwar PDP, ya ce wahalallu masu son cigaba da wahala ne zasu yi tunanin ƙara amince wa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262