Tsohuwar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Edo Ta Fice daga Jam'iyyar APC

Tsohuwar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Edo Ta Fice daga Jam'iyyar APC

  • Tsohuwar shugabar Majalisar dokokin jihar Edo, Misis Elizabeth Ativie, ta tabbatar da ficewarta daga jam'iyyar APC
  • Misis Ativie tace ba wai rashin nasarar samun tikitin takara ya sa ta ɗauki matakin ba, ta yi haka ne saboda rikici da watsar da mata
  • Wannan lamari na zuwa ne a dai-dai lokacin da APC ke kokarin shawo kan fusatattun mambobinta domin shirya zuwan 2023

Edo - Tsohuwar kakakin majalisar dokokin jihar Edo, Misis Elizabeth Ativie, ta yi murabus daga kasancewarta mamba a jam'iyyar APC, ta kafa hujja da rashin ba mata muƙamai.

Jaridar Punch ta tattaro cewa tsohuwar 'yar majalisar ta sanar da matakin ne a wani taron manema labarai da ya gudana a Cibiyar 'yan jarida dake Hedkwatar NUJ reshen jihar Edo.

Kara karanta wannan

Hotuna: Lamiɗo, Da Wasu Yan Takarar Gwamna 16 Na Jam'iyar PDP Sun Sa Labule da Wike

Haka nan ta rubuta wasika mai ɗauke da adireshin shugaban APC na Edo, Kanal David Imuse (Mai ritaya.), ta hannun shugaban jam'iyya na gundumar Irhue ta huɗu da shugaban ƙaramar hukumar Uhunmwonde.

Tsohuwar kakakin majalisar dokokin Edo, Elizabeth Ativie.
Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Edo Ya Fice daga Jam'iyyar APC Hoto: Elizabeth Ativie
Asali: Facebook

A cikin wasikar da ta rubuta, Misis Ativie tace, "Na rubuta wannan takarda ne domin sanar da kai a hukumance cewa na yi murabus daga jam'iyyar APC kuma nan take."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Dalilin ɗaukar wannan matakin na da alaƙa da rikicin cikin gida da yaƙi ci ya ƙi cinyewa a reshen ƙaramar hukumar Uhunmwonde da jihar Edo baki ɗaya."
"Na yi tsammanin ina da alfarmar na shiga Sakatariyar APC kuma na fita a lokacin da nake so amma abun mamaki Ma'aikata suka garƙame ƙofa, suka ce ba inda za ni. Na faɗa musu mutane na jira na dan haka ya kamata na tafi."

Kara karanta wannan

Tsoho Ministan Ya Fallasa Wani Sirri, Ya Faɗi Abu Ɗaya Da Zai Sa Yan Najeriya Su Zaɓi APC a 2023

Ko fitarta APC na da alaƙa da rashin nasara a zaɓen fidda gwani?

The Nation tace a jawabin da ta yi, Tsohuwar shugabar majalisar ta cigaba da cewa, "Ina sanar da ɗumbin magoya baya na da ɗaukacin al'umma cewa na fice daga tsohuwar jam'iyyata watau APC."

"Na yanke haka ne sakamakon rikicin da ya baibaye jam'iyyar tun bayan kammala zaɓen fidda gwani, rashin demokaraɗiyyar cikin gida da kuma damar da aka ba wasu suka babbake komai a APC."
"Ban ɗauki wannan matakin saboda rashin nasarar lashe tikitin takarar kujerar mamba mai wakiltar mazaɓar Uhunmwonde/Orhionwwon a majalisar wakilai ta ƙasa ba, kowa yasan ni yar fafutuka ce, ina yaƙi don ganin mata sun shiga ana dama wa da su."

A wani labarin kuma Lamari Ya Kara Dagule Wa APC, Ɗaruruwan Mambobinta Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar PDP

Yayin da rage sauran 'yan watanni a fafata zaɓen 2023, jam'iyyar APC mai mulki ta gamu da babban cikas a jihar Ondo.

Kara karanta wannan

2023: 'Yan Bindiga Sun Buɗe Wa Mutane Wuta a Wurin Taron Jam'iyyar Siyasa, Sun Aikata Ɓarna

Daruruwan mambobin APC a ƙaramar hukumar Ifedore sun tattara sun koma jam'iyyar PDP a wurin wani taro yau Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262