2023: Ɗaruruwan Mambobin APC Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar PDP a Jihar Ondo
- Yayin da rage sauran 'yan watanni a fafata zaɓen 2023, jam'iyyar APC mai mulki ta gamu da babban cikas a jihar Ondo
- Daruruwan mambobin APC a ƙaramar hukumar Ifedore sun tattara sun koma jam'iyyar PDP a wurin wani taro yau Litinin
- Shugaban PDP a yankin, Chief Dare Owolafe, yace wannan cigaban abin murna ne da farin ciki don shirya zuwan babban zaɓe
Ondo - Watanni gabanin babban zaɓen 2023, ɗaruruwan mambobin All Progressives Congress (APC) mai mulki a ƙaramar hukumar Ifedore, jihar Ondo sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP.
Jaridar Punch tace an gudanar taron karɓan masu sauya shekan a Sakatariyar PDP dake Igbara-Oke, hedkwatar ƙaramar hukumar ranar Litinin wato yau.
Taron ya samu halartar jiga-jigan jam'iyyar PDP a matakin ƙaramar hukuma da jiha. Da yake maraba da masu sauya shekan, shugaban PDP na ƙaramar hukumar Ifedore, Chief Dare Owolafe, ya tabbatar musu da an zama ɗaya.
Yace kasancewar sun shiga tsagin adawa, za'a musu adalci, kuma sun zama ɗaya da sauran mambobi, ya kuma yi kira ga sauran 'yan siyasa su rungumi PDP wacce ya kira da 'Jam'iyya mai nasara.'
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A kalamansa ya ce:
"Mun yi farin cikin dawowar mambobin APC zuwa cikin mu, muna da yaƙinin hakan zai ƙara mana kwarin guiwa, wannan cigaba ne da ake maraba da shi."
Wajibi mu tashi tsaye wajen kawar da APC a 2023 - Faboyede
Tsohon shugaban jam'iyyar da ya sauka, Mr Clement Faboyede, ya bayyana lamarin da wani cigaba da ya buɗe sabon shafi, inda yace dama an yi tsammanin tururuwar sauya sheka daga APC.
"Dukkan mu shaidu ne cewa ba sauki a Najeriya game da tsaro ko Ilimi, 'ya'yan mu maza da mata sun kwashe sama da watanni Shida a gida saboda yajin aikin ASUU, a zahirance gazawar gwamnati ne."
"Ba zamu lamurci cigaba da rayuwa a haka ba, gwamnatin APC ta yi mummunar gazawa. Lokacin Mulkin Jonathan mun san yadda ƙasa take kuma yanzu ma muna ganin yadda lamari ke tafiya a ƙasa."
"Wannan ne yasa muke ganin lokaci ya yi da zamu kawar da APC a zaɓen 2023, ya kamata 'yan Najeriya su farga, su kawo karshen mulkin APC tun daga matakin gunduma har zuwa ƙasa."
A wani labarin kuma Rikici Ya Ɓalle a APC, Wani Ɗan Takarar Gwamna Ya Yi Watsi Da Kuɗin Yakin Neman Zaɓen Tinubu a 2023
Rikicin jam'iyyar APC na neman taɓa shirin Kamfe a wasu jihohi, jihar Enugu ta nemi kada a tura mata kudin Kamfen na Tinubu.
Ɗan takarar gwamna a jihar Enugu karkashin APC yace ana tsammanin kuɗin ka iya wargaza jam'iyyar idan aka zo batun raba su.
Asali: Legit.ng