Jigon APC Da Dubbannin Magoya Bayansa Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a Ogun
- Na hannun daman tsohon gwamnan Ogun kuma jigo a APC ya tattara masoyansa sun koma jam'iyyar PDP
- Babatunde Onakoya, yace bisa tilas aka masa kora da hali saboda yawan rikici da yaƙi karewa a jam'iyya mai mulki
- Shugaban PDP reshen Ogun yace kullum mutane kara tururwar shiga jam'iyyar suke saboda sun yanke watsar da APC a 2023
Ogun - Wani jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Ogun, Babatunde Onakoya, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP tare da dubbanin magoya bayansa.
Onakoya, na hannun daman tsohon gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, wanda ya shahara da sunan, Debasco, ya jagoranci tafiyarsa ta siyasa da ake kira tawagar siyasar Debasco zuwa PDP.
Punch ta rahoto cewa Onakoya da ɗumbin masoyansa sun tabbatar da sauya shekarsu a hukumance ne a wani taro da aka shirya a gidansa Atiba dake Ijebu Ode ranar Laraba.
Ya bayyana cewa tilas aka masa ya bar jam'iyya mai mulki saboda rikicin cikin gida ya baibayeta kuma aka gaza lalubo bakin zaren.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ɗan siyasan, wanda ya yi amfani da bikin cikarsa shekaru 69 wajen sanar da shigarsa PDP, yace duk da Amosun da gwamna Dapo Abiodun 'yan uwansa ne, ba shi da wani da ya wuce tattara kayansa ya bar APC a halin rikicin da take ciki.
Yan Najeeiya sun yanke hukunci game da 2023
Da yake jawabi gabanin miƙa tutar PDP ga Onakoya, shugaban PDP na Ogun, Sikirulahi Ogundele, ya bayyana cewa kullum mutane ƙara tururuwa suke suna shiga tsagin adawa.
A cewar Ogundele, ranar Jumu'an nan da ta gabata mutum 10,000 suka sauya sheka zuwa PDP, inda ya ƙara da cewa tun kafin zuwan 2023, mutane sun yanke shawarar kawo karshen wahalar rayuwa ta hanyar watsi da APC.
Bugu da kari, ya ayyana Onakoya a matsayin wani babban kifi da PDP ta kamo kuma fitaccen jagoran siyasa a shiyyar Ogun ta gabas wanda ya shiga jam'iyyar adawa da masoya sama da 5,000.
A wani labarin kuma Jigon APC Ya Fallasa Babban Abinda Tinubu Ke Tsoro Game Da Atiku, Kwankwaso a 2023
Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa reshen shiyyar arewa maso yamma, Salihu Lukman, ya amince da gaskiyar cewa Bola Tinubu, ba wani sananne bane idan ana batun zaɓen shugaban kasa a Najeriya.
A wata hira ta bayan fage da Jaridar This Day, Lukman ya bayyana cewa karo na karshe da Tinubu ya fito a takardar kaɗa kuri'a shi ne a zaɓen 2003 ba kamar Atiku Abubakar , da Peter Obi ba.
Asali: Legit.ng