Rikicin PDP: Dole Shugaban Jam'iyya Ya Yi Murabus, Jigon PDP Ya Koma Bayan Wike

Rikicin PDP: Dole Shugaban Jam'iyya Ya Yi Murabus, Jigon PDP Ya Koma Bayan Wike

  • Chief Olabode George, jigo a jam'iyyar PDP ya ce wajibi shugaban jam'iyya na ƙasa, Dakta Ayu, ya yi murabus
  • George ya bayyana cewa matukar ana son a yi adalci bai kamata shugaban jam'iyya, shugaban BoT, ɗan takarar shugaban ƙasa su fito daga yanki ɗaya ba
  • Rikicin jam'iyyar PDP na ƙara tsanani game da kiran da ake Iyorchia Ayu, ya yi murabus kamar yadda ya ɗau alƙawari

Rivers -Jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Chief Olabode George, yace ya zama wajibi shugaban jam'iyya na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya tattara kayansa ya bar Ofis gabanin fara yakin neman zaɓe.

A jadawalin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta tsara na babban zaɓen 2023, jam'iyyun siyasa zasu fara kamfe a ranar 28 ga watan Satumba, 2022, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamna Wike Ya Yi Barazanar Taimaka Wa Atiku Ya Sha Kaye a Zaben 2023

Gwamna Wike da Chief Olabode George.
Rikicin PDP: Dole Shugaban Jam'iyya Ya Yi Murabus, Jigon PDP Ya Koma Bayan Wike Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Da yake jawabi a Patakwal, babban birnin jihar Ribas ranar Alhamis (yau), George, yace rashin adalci ne manyan masu faɗa aji uku na jam'iyya su fito daga yanki ɗaya.

A cewarsa, rashin adalci ne shugaban jam'iyya na ƙasa, ɗan takarar shugaban ƙasa da shugaban kwamitin amintattu BoT na jam'iyyar PDP su fito daga yanki guda.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda za'a magance rikicin kafin zaɓe - George

Chief Olabode George ya kara da cewa matakin da ya dace a ɗauka a yanzun don shawo kan matsalar shi ne Ayu ya yi murabus daga muƙaminsa tun kafin a kaɗa gangar yakin neman zaɓe.

A cewarsa, illa ce mai girma babbar jam'iyyar hamayya ta shiga fagen fafata yakin neman zaɓe kawunan 'ya'yanta na rarrabe.

Yace abinda Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, yake bukatar a yi yana kan dai-dai, idan har ana son yin adalci, zaman lafiya da haɗin kai a ham'iyya.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Tsananta: Butulci da Girman Kai Ba Zasu Kaika Ko Ina Ba, Wike Ya Caccaki Shugaban PDP

Gwamna Wike ne a sahun gaba daga cikin jiga-jigan jam'iyya dake kokarin ganin Ayu ya tattara kayansa ya bar muƙaminsa na shugaban PDP.

A wani labarin kuma Jigon APC Ya Fallasa Babban Abinda Tinubu Ke Tsoro Game Da Atiku, Kwankwaso a 2023

Bola Tinubu bai shahara a matakin zaɓen kasa ba idan aka kwatanta shi da yan takarar shugaban kasa na jam'iyyun PDP, NNPP da LP.

Mataimakin shugaban APC na shiyyar arewa maso yamma, Dr. Salihu Lukman, shi ne ya ayyana amince wa da batun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel