Jerin Sunayen Jiga-Jigan PDP Na Kasa Dake Rura Wutar Rikicin Atiku da Wike

Jerin Sunayen Jiga-Jigan PDP Na Kasa Dake Rura Wutar Rikicin Atiku da Wike

  • Ana zargin tsoffin gwamnoni biyu daga jihohin Ondo da Kuros Riba da jagorantar rura wutar rikicin Atiku Abubakar da gwamna Wike
  • Bayan su kuma ana zargin wasu tsofaffin Ministoci, wani Sanata da masu ruwa da tsaki a PDP da ƙara wutar rikicin Fetur
  • Sai dai bayanai sun nuna cewa mafi yawan waɗan da ake zargin suna cikin tawagar sulhu na tsagin gwamna Wike

Wasu masu ruwa da tsaki a jam'iyyar PDP sun bayyana cewa suna zargin wasu jiga-jigai da hannu a rikicin da ya jima tsakanin Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas.

The Nation ta ruwaito cewa waɗan da ake zargin mafi yawansu suna cikin kwamitin sulhun da aka kafa domin lalubo hanyar maslaha tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa da gwamnan Ribas amma suka gaza.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa da Wani Minista Sun Yi Yunkurin Mana Karfa-Karfa a Zaben Jihata, Gwamna Ya Tona Asiri

Atiku Abubakar da gwamna Wike.
Jerin Sunayen Jiga-Jigan PDP Na Kasa Dake Rura Wutar Rikicin Atiku da Wike Hoto: Nyesom Wike, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Jerin Sunayen Jiga-Jigan PDP da Ake zargi da rura wutar rikicin

1. Tsohon ministan yaɗa labarai, Farfesa Jerry Gana.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

2. Tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko.

3. Tsohon Antoni Janar Na ƙasa, Mohammed Adoke.

4. Sanata daga jihar Ribas, Olaka Nwogu.

Kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) ya fara shirye-shiryen ziyartar gwamnonin jam'iyyar PDP dake goyon bayan Wike da nufin kawo ƙarshen matsalar da ta ƙi ƙare wa, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Gwamnonin sun haɗa da gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, gwamna Ikpeazu Okezie na jihar Abia da kuma gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom.

PDP ta rasa zaman lafiya a cikin gida ne tun bayan kammala zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa, wanda Atiku ya lallasa Wike da sauran yan takara a watan Mayu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Sa Labule da Wasu Gwamnoni a Aso Rock, Hotuna

Sakamakon zaɓen ya fusata gwamna Wike wanda ya tsame kansa daga duk wasu harkokin jam'iyya. Lamarin ya ƙara tsananta bayan ayyana gwamna Ufeanyi Okowa na jihar Delta a matsayin abokin takarar Atiku.

A wani labarin kuma Jigon APC Ya Fallasa Babban Abinda Tinubu Ke Tsoro Game da Atiku da Kwankwaso

Bola Tinubu bai shahara a matakin zaɓen kasa ba idan aka kwatanta shi da yan takarar shugaban kasa na jam'iyyun PDP, NNPP da LP.

Mataimakin shugaban APC na shiyyar arewa maso yamma, Dr. Salihu Lukman, shi ne ya ayyana amince wa da batun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262