Mutanen Jihar Ribas Ne Suka Dakile Yunkurin Sa Hannu a Zaben 2019, Wike
- Gwamna Wike na jihar Ribas ya nuna gamsuwarsa da matakin shugaban ƙasa na tsame kansa daga zaɓen 2023 dake tafe
- Gwamnan ya ce alƙawarin Buhari da kokarinsa na gudanar da sahihim zaɓe abun a yaba ne, amma a 2019 sun yi yunkurin shiga zaɓen Ribas
- Tun bayan dawowarsa daga Landan, Wike na ci gaba da tsokaci kan lamurrra da dama da suka shafi siyasar Najeriya musamman rikicin PDP
Rivers - Gwamna Nyesom Wike ya zargi shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ɗa tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, da yunkurin tsoma baki a a zaɓen 2019 amma mutane jihar Ribas suka dakile shirin.
Wike ya yi wannan furucin ne a ƙaramar hukumar Ikwerre lokacinda ya kaddamar da fara aikin gina hanyoyin Igwuruta Internal, kamar yadda Channels ta ruwaito.
A cewar ƙusan jam'iyyar PDP, 'yan Najeriya zasu sha mamaki game da sakamakon zaɓen 2023 matukar hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta gudanar da sahihin zaɓe.
A kalamansa ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Matsalata INEC, ban sani ba ko zasu tabbatar da maganganunsu saboda alƙawari suke ta ɗauka a yanzu, ban sani ba ko zasu cika alƙawurransu. Idan INEC zata cika alkawarinta ga yan Najeriya na gudanar da sahihin zaɓe, zan ji daɗi."
Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa shugaban ƙasa Buhari ya yi alƙawarin ba zai bar wata barazana ko ba da tsoro da zata gurbata zaɓen 2023 ba kuma ba zai yi katsalandan ba.
Da yake tsokacin kan kalaman Buhari, gwamna Wike ya gode wa shugaban kasan bisa ɗaukar alƙawarin ba zai shiga ya yi kane-kane a zaɓe mai zuwa ba.
"Lokacin da shugaban kasa yace ba zai yi katsalandan ba (A zaɓe), ya gaya wa gwamnoni, ba zai tsoma baki ba, sai nake tambaya, shin sauran ka tsoma baki? Ka shiga mana ta hanyar turo jami'an tsaro su gama da mu a nan Ribas."
Kun so shiga zaɓen mu a 2019 - Wike
Gwamnan wanda ya nuna jin daɗinsa da matakin shugaban kasa, ya ce a zaɓen 2019 da ya gabata an so shiga a murɗe musu zaɓen jihar Ribas.
"Nagode wa shugaban ƙasa da ya fito fili ya gaya wa gwamnonin ba zai tsoma baki ba saboda a baya ya yi yunkurin shiga da Sojoji ta hannun tsohon ministan Sufuri, mutane suka tashi tsaye suka hana faruwar shirin."
"Ina ƙara gode wa shugaban kasa domin yana son barin kyakkyawan aiki na gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe."
A wani labarin kuma Bola Tinubu Da Jiga-Jigan APC Sun Nemi Wata Alfarma Ɗaya Daga Wurin Jonathan
A kokarin cika burinsa na zama shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Tinubu, ya samu rakiyar abokin takararsa, Kashim Shettima, da wasu gwamnoni, ya nemi goyon bayan Jonathan a 2023.
Asali: Legit.ng