Gwamnatin Ebonyi Zata Rantsar Da Ciyamomi Duk Da Kotu Ta Soke Zaben

Gwamnatin Ebonyi Zata Rantsar Da Ciyamomi Duk Da Kotu Ta Soke Zaben

  • Gwamnatin jihar Ebonyi ta ci gaba da shirin rantsar da shugabannin kananan hukumomi duk da hukuncin Kotu
  • A ranar 25 ga watan Agusta, Babbar Kotun tarayya ta yanke hukuncin soke zaɓen baki ɗaya saboda saɓa wa doka
  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Ebonyi ta ayyana 'yan takarar APC mai mulkin jihar a matsayin waɗan da suka yi nasara a dukkan kujeru

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ebonyi - Gwamnatin jihar Ebonyi na shirye-shiryen rantsar da sabbin shugabannin ƙananan hukumomi 13 dake faɗin jihar duk da sanin cewa Kotu ta soke zaɓen da aka yi.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ta lashe baki ɗaya kujerun ciyamomi 13 da Kansiloli 171 dake sassan jihar.

Tun farko an tsara ba zaɓaɓɓun shugabannin rantsuwar kama aiki ne ranar 1 ga watan Satumba, 2022 gabanin babbar Kotun tarayya dake zama a Abakaliki, ta soke zaɓen a ranar 25 ga watan Agusta, 2022.

Kara karanta wannan

Jigawa: Adadin Mutanen Da Suka Mutu a Ambaliyar Ruwa Ya Ƙaru, Ya Haura Mutum 50

Gwamna jihar Ebonyi, David Umahi.
Gwamnatin Ebonyi Zata Rantsar Da Ciyamomi Duk Da Kotu Ta Soke Zaben Hoto: Premiumtimesng
Asali: UGC

Kotun ta bayyana cewa wa'adin mulkin Ciyamomi da Kansilolin dake kan madafun iko zai kare ne a watan Agusta na shekara mai zuwa 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka zalika Kotun ta haramta wa gwamnatin jiha naɗa shugabannin riko wato Kantomomi da zasu tafiyar da harkokin gwamnatin ƙananan hukumomin.

Duk da haka, shugaban APC reshen jihar Ebonyi, Stanley Emegha, a ranar Litinin, ya jaddada cewa Ciyamomi 13 da Kansiloli 171 da mutane suka zaɓa, wajibi ne a ba su rantsuwar kama aiki a ranar 1 ga watan Satumba kamar yadda aka tsara.

Hukuncin Kotu bai soke zaɓe ba - Kwmaishina

A ɓangaren gwamnati, kwamishinan yaɗa labarai, Uchenna Orji, yayin zantawa da Channels tv, ya ce hukuncin da Kotu ta yanke bai warware zaɓen da aka gudanar ba.

Kwamishinan ya ƙara da bayanin cewa Kotu ba ta hana rantsar da sabbin shugabannin da al'umma suka zaɓa ba.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kotun Tarayya Ta Sake Daƙile Bukatar Belin Abba Kyari da Wasu Mutum Hudu

Kansiloli sun karɓi hukuncin Kotu

Sai dai Kansiloli 171 da Allah ya ba mulki a zaɓen wanda ya gudana a watan Yuli, sun bayyana cewa sun karɓi hukuncin da Kotu ta yanke hannu bibbiyu.

A wata sanarwa da suka fitar ranar Litinin, Kansilolin sun amince da hukuncin babbar Kotun tarayya, kana sun sha awashin cigaba da goyon bayan gwamnatin jiha.

Haka nan kuma sun roki gwamnatin jihar ta Ebonyi ta amince da hukuncin da Kotu ta yanke kuma ta yi biyayya.

A wani labarin kuma Gwamna Wike Ya Yi Martani Ga Wasu Jiga-Jigan PDP, Ya Bayyana Aikin Da Yake Wa APC

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesome Wike, ya caccaki wasu 'ya'yan PDP dake sukarsa, ya nemi su maida hankali kan cin zabe.

Wike ya bayyana cewa shi da 'yan tawagarsa sun maida hankali wajen ganin bayan APC reshen jihar Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel