Bola Tinubu Ya Nemi Alfarma Daya a Wurin Jonathan Kan Zaben 2023

Bola Tinubu Ya Nemi Alfarma Daya a Wurin Jonathan Kan Zaben 2023

  • A kokarin cika burinsa na zama shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan
  • Tinubu, ya samu rakiyar abokin takararsa, Kashim Shettima, da wasu gwamnoni, ya nemi goyon bayan Jonathan a 2023
  • Wannan na zuwa ne makonni bayan tsohon gwamnan Legas ya gana da Obasanjo har gida a jihar Ogun

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Mai neman kujerar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonthan a Abuja a wani ɓangare na ci gaba da ziyarar neman goyon baya gabanin 2023.

Duk da ba'a bayyana abinda suka tattauna ba, amma wata majiya daga cikin tawagar Tinubu ta shaida wa wakilin Punch cewa ziyarar wani ɓangare ne na ƙara faɗin neman shawari daga masu ruwa da tsaki a harkar siyasa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jonathan Ya Yi Ƙus-Ƙus Da Tinubu, Shettima Da Gwamnonin APC A Abuja, Hoto Ya Bayyana

Ziyarar Jiga-Jigan APC ga Jonathan.
Bola Tinubu Ya Nemi Alfarma Daya a Wurin Jonathan Kan Zaben 2023 Hoto: punchng
Asali: Twitter

Majiyar ta bayyana cewa yayin ziyarar Bola Tinubu ya nemi alfarmar goyon baya daga wurin tsohon shugaban ƙasa.

"Bai kamata ziyarar da Tinubu ya kaiwa Jonathan ta zama abun mamaki ba, Tinubu ya zauna lafiya da kowane ɗan siyasa a cikin jam'iyya ko a tsagin masu adawa." inji majiyar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka nan majiyar ta ƙara da cewa Jonathan ya ji daɗin ganin mutanen da suka kai masa ziyarar kuma ya nuna kofarsa a buɗe take ya ba da shawari kan cika burin ɗan takarar shugaban kasan.

Ɗan takarar Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, da wasu gwamnonin APC sun samu halartar taron.

Wannan na zuwa ne biyo bayan ziyarar da Bola Tinubu ya kai wa tsohon shugaban kasa, Chief Olusegun Obasanjo, har gida a Abeokuta, jihar Ogun.

Babu rikici tsakanin Tinubu da Adamu - NWC

Kara karanta wannan

2023: Cikakken Bayanin Yadda Tinubu Ya Ki Amincewa Da Bukatun Wike A Landan Ya Bayyana

A wani cigaban kuma, kwamitin gudanarwa na APC ta ƙasa (MWC) ya yi fatali ɗa raɗe-raɗin da ake yaɗa wa cewa alaƙa ta yi tsami tsakanin Bola Tinubu da shugaban jam'iyya na ƙasa, Abdullahi Adamu.

NWC ya ce babu wani saɓani tsakanin mutanen biyu kan zaɓen Gwamna Simon Lalong a matsayin Dataktan Kamfe da kuma Festus Keyamo a matsayin kakaki.

A wani labarin kuma Gwamnatin Ebonyi Zata Rantsar Da Ciyamomi Duk Da Kotu Ta Soke Zaben da APC ta lashe

Gwamnatin jihar Ebonyi ta ci gaba da shirin rantsar da shugabannin kananan hukumomi duk da hukuncin Kotu.

A ranar 25 ga watan Agusta, Babbar Kotun tarayya ta yanke hukuncin soke zaɓen baki ɗaya saboda saɓa wa doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164