Tinubu ne ‘Dan takara Mafi Cancanta, Amma Akwai Abin da Nake Tsoro - Shugaban APC

Tinubu ne ‘Dan takara Mafi Cancanta, Amma Akwai Abin da Nake Tsoro - Shugaban APC

  • Salihu Lukman wanda shi ne shugaban APC a shiyyar Arewa maso yamma yana ganin Bola Tinubu ya sha gaban kowa a 2023
  • Dalilin ‘dan siyasar na cewa haka shi ne Bola Tinubu bai taba sauya-sheka saboda bai samu takara a wata jam’iyyar siyasa ba
  • Irinsu Peter Obi, Atiku Abubakar, da Rabiu Kwankwaso duk sun saba tsalle-tsalle da zarar ba su samu abin da suke nema ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyya Arewa maso yamma, Salihu Lukman ya zanta game d zaben 2023 da kuma ‘dan takararsu.

A wata hira ta musamman da Punch tayi da shi, Salihu Lukman ya bayyana Bola Tinubu a matsayin ‘dan takaran da ya fi takwarorinsa mutunci.

Lukman yace watakila a sauran masu takararar a samu wanda ya dace irin Bola Tinubu, amma a cewarsa ‘dan takaransu ya fi dukkansu kima.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPP Ya Fadi Babban Abin da Ya Wargaza Taron Dangin Kwankwaso/Obi

Abin da ya sa Tinubu yake da kima a idanun jama’a da gaskiya shi ne tsayin dakarsa wajen zama a jam’iyya daya, akasin sauran masu neman mulki.

Tsilla-tsillar 'yan takaran 2023

Atiku Abubakar ya yi tsalle-tsalle daga PDP zuwa ACN zuwa PDP, daga baya ya koma APC kafin ya sake dawowa jam’iyyar PDP da yake takara a yau.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka zalika Peter Obi ya yi jam’iyyun APGA, PDP da LP. Shi kuma Rabiu Musa Kwankwaso ya yi yawo tsakanin APC da PDP, yanzu yana NNPP.

Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

“’Dan takaranmu da abokin takararsa shi ne kurum wanda bai taba canza jam’iyya domin neman takara ba. Kan na nufin su mutane ne masu daraja.”
“Abin da wannan yake nufi shi ne za a iya damka masu amana fiye da mutanen da nan-take suke canza jiha da zarar ba sus amu abin da suke nema ba."

Kara karanta wannan

An Raba Kan Shugabannin PDP da Batun Tunbuke Shugaban Jam’iyya daf da 2023

- Salihu Lukman

Tsoro na idan APC ta ci zabe - Salihu Lukman

Da ‘yan jarida suka tambaye shi a game da abubuwan da za su taimakawa APC da inda jam’iyyar za ta samu rauni, sai ya nuna wajen cika alkawuranta.

Salihu yake cewa idan jam’iyyar APC ta zarce a kan mulki a 2023, babban abin da yake tsoro shi ne yadda za ta kara karfi domin ta cigaba da lashe zabuka.

“Na fada kuma har yanzu ina fada, abin da muke bukata a jam’iyyar APC shi ne mu duba alkawuran da muka tsakanin shekarar 2015 da 2019.”
“Ina ne aka samu gibi, kuma shakka babu akwai gibi. Me ake bukatar ayi domin a cike wadannan gibi?”

- Salihu Lukman

An ji Salihu yana mai cewa ya yarda APC tana fama da wasu kalubale a matsayinta na jam’iyya.

Sabawa dokar zaben 2022

An ji labari cewa dokar zabe ta shekarar 2022 ba ta yarda wani yayi amfani da coci ko masallatai wajen yakin neman zabe ko a tallata wata tafiyar siyasa ba.

Kara karanta wannan

Daga karshe Atiku Abubakar ya yi maganar ‘rigimarsa’ da Gwamna Wike a PDP

Kwamishinan INEC, Festus Okoye yace duk wanda ya yi hakan ya saba dokar kasa, kuma za a iya daure shi a kurkuku ko akalla ya biya tarar N1m zuwa N2m.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng