Sauya Sheka: Atiku Abubakar, Ayu da Wasu Jiga-Jigan PDP Sun Dira Birnin Kano
- Atiku Abubakar, Shugaban PDP, tsohon gwamnan Jigawa da wasu jiga-jigai sun dira birnin Kano da yammacin ranar Lahadi
- Ɗan takarar shugaban kasan da ƴan tawagarsa sun kai ziyara Kano ne domin karɓan Sanata Ibrahim Shekarau zuwa PDP
- Malam Shekarau ya samu sabani da jam'iyyar NNPP mai kayan marmari watanni bayan ficewa daga APC
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kano - Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, Shugaban jam'iya na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, da wasu jiga-jigan PDP sun dira birnin Kano.
Tsohon matamakin shugaban kasan ne ya bayyana haka shafinsa na dandalin sada zumunta Tuwita da yammacin yau Lahadi.
Atiku ya kai ziyarar jihar ne domin tarban tsohon gwamnan jihar na tsawon zango biyu, Sanata Ibarhim Shekarau, zuwa jam'iyyar PDP.
Da yake tabbatar da isarsa Kano a shafinsa na Tuwita tare da Hotuna, Atiku ya rubuta cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Yanzu na dira a cibiyar kasuwanci, watau jihar Kano. Kwanaki masu zuwa zasu kasance masu amfani sosai."
Yasuhe za'a bikin tarbar Shekarau?
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa manyan masu faɗa aji na jam'iyyar PDP zasu yi wa Shekarau wankan shiga jam'iyyar a hukumancen ranar Litinin, 29 ga watan Agusta, 2022.
Shekarau, Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar Dattawan Najeriya, ya ɗare kan kujerar ne karakashin APC daga bisani ya sauya sheka zuwa NNPP bayan samun saɓani da gwamna Ganduje.
Watanni kaɗan bayan haka, alaƙar Shekarau da jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Kwankwaso, ta yi tsami biyo bayan gaza bai wa mutanen Sanatan tikitin takara a 2023.
Hotunan isar su Atiku Kano
A wani labarin kuma Obasanjo Ya Sa Labule Da Tsofaffin Shugaban Ƙasa Biyu, Ya Yi Magana Kan Wanda Zai Gaji Buhari a 2023
Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ziyarci IBB da Janar Abdulsalmi Abubakar a Minna, jihar Neja ranar Lahadi.
Obasanjo ya bayyana cewa ba shi da wani ɗan takarar shugaban ƙasa da yake goyon baya, ajendar ƙasa ya sa a gaba.
Asali: Legit.ng