2023: Ɗan Takarar Gwamna A PDP Ya Fice Daga Jam'iyyar, Ya Samu Tikitin Takara a 2023
- Wani da ya nemi tikitin takarar gwamnan Ogun a inuwar PDP ya nuna fushinsa a fili, ya sauya sheƙa zuwa PRP
- Farfesa Olufemi Bamgbose, ya samu tikitin takarar gwamna a sabuwar jam'iyyarsa da zai ba shi damar shiga zaɓen 2023
- Ɗan takarar ya bayyana yadda shugabannin PDP suka yaudare shi suka raba shi da ƴan kuɗaɗensa
Ogun - Farfesa Olufemi Bamgbose, wanda ya nemi tikitin takarar gwamnan Ogun a PDP ya fice daga jam'iyyar, ya koma jam'iyyar People’s Redemption Party (PRP) kuma an ba shi tikitin gwamna a 2023.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban jam'iyyar PRP na jihar Ogun, Mista Samson Ogunsanya, shi ne ya bayyana haka ranar Asabar a Abeokuta.
A wurin taron manema labarai, Ogunsanya, ya ayyana Farfesa Bamgbose a matsayin ɗan takarar gwamnan Ogun karkashin inuwar PRP a zaɓen 2023.
A kalamansa ya ce, "Mun amince da ɗora Farfesa Olufemi Bamgbose a matsayin ɗan takara ne saboda dabarun lashe zaɓe, yana da tarihi mai kyau, yana da komai zai iya kai labari."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Meyasa ya yanke barin PDP?
Da yake jawabi kan maƙasudin sauya sheƙarsa daga PDP zuwa PRP, Bamgbose ya koka kan yadda tsohuwar jam'iyyarsa ta fusata shi.
Ya ce lokacin yana PDP ya hakura da burinsa na takarar gwamna ya barwa ɗan takarar da aka tsayar, Oladipupo Adebutu, sannan ya koma ya karɓi Fam din takarar Sanatan Ogun ta yamma.
Farfesa Bamgbose ya ce ya lashe Zaɓen fidda gwani amma abun mamaki sai ga shi shugabannin jam'iyya sun sauya sunan shi da wani daban.
Ya ƙara da cewa rashin ɗaukar mutane da muhimmanci da rashin haɗin kan jam'iyyar ya sa ya tattara kayansa zuwa PDP, jam'iyyar da a cewarsa ta fi sahihanci da zama abin dogaro.
Bamgbose ya ce ya yi danasanin abubuwan da suka faru bayan PDP ta karɓi maƙudan kudade a hannunsa domin saya masa Fom ɗin Sanata.
A cewarsa, bayan duk abinda ya faru ya riga da ya faru, shugabancin PDP ya rubuto masa takardar tausasa zuciya da neman yafiya, tare da alƙawarin rama masa amma ta gaza cika wa.
Farfesan ya bayyana jam'iyyar PDP reshen jihar Ogun a matsayin mai cin hanci da rashawa kuma mara son gaskiya da adalci ga ƴaƴanta.
A wani labarin kuma Daga Karshe, Malam Ibrahim Shekarau Ya Yanke Jam'iyyar da Zai Koma Bayan Fita NNPP
Tsohon gwamnan Kano ya amince ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP kuma Atiku da kansa zai karɓe shi yau Lahadi.
Shugaban PDP, Shehu Wada Sagagi, ya ce shirye-shirye sun yi nisa na zuwan Atiku da kuma dawowar Malam Ibrahim Shekarau.
Asali: Legit.ng