Mijina Ne Zai Lashe Zaben Gwamnan Jihar Bauchi a 2023, Sadiya Farouk
- Ministar harkokin jin kai da walwala, Hajiya Sadiya Farouq, ta ce idan Allah ya so mijinta ne gwamnan jihar Bauchi na gaba a 2023
- Hajiya Sadiya, Minista mafi karancin shekaru a gwamnatin Buhari, ta ce Sadique Abubakar mutum ne da kowa zai so ya zama gwamna
- Sai dai Ministar da kuma mijinta tsohon hafsan sojin sama na fuskantar suka daga wasu ƙungiyoyin APC a Bauchi
Bauchi - Ministar jin ƙai da walwalar al'umma, Hajiya Sadiya Farouq, ta bayyana kwarin guiwarta cewa mutane zasu dangwala wa Mijinta, Air Marshal Sadique Abubakar (mai ritaya.), ya lashe zaɓen gwamnan Bauchi a 2023.
Punch ta rahoto cewa Ministar ta yi wannan furucin ne yayin da take kwarzanta nagartar mijinta a wurin wani taron ƴan asalin Bauchi da abokan tsohon hafsan Sojin wanda ya gudana a Abuja.
Yayin da take jawabin maraba, Ministar ta bayyana shi da ɗan uwa da babu kamarsa, Mijinta kuma irin gwamnan da kowa ne mutum ke Alla-Allah ya samu a jiharsa.
Sadiya ta ce, "Sadique babban ɗan uwa ne, aboki kuma Mai gidana, ba ni da tantamar cewa zai zama gwamnan Bauchi da ba'a taɓa yin kamarsa Insha Allah."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sadiya Farouq, Minista mafi ƙarancin shekaru karkashin wannan gwamnatin, ta rike kujerar ma'ajiyi na jam'iyyar CPC kafin a rusheta zuwa maja data haifar da jam'iyyar APC.
Kalubalen da take fuskanta a Bauchi
Wannan cigaban na zuwa ne watanni uku bayan wata kungiyar magoya bayan APC ƙarƙashin inuwar Coalition of APC Groups’ ta zargi Ministar da saye Deleget su zaɓi Abubakar tun kafin zaɓen fudda gwani.
Shugaban ƙungiyar, Yusuf Ajayi, shi ne ya yi wannan zargin a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Bauchi ranar 23 ga watan Mayu, 2023.
Ajayi ya yi zargin cewa maimakon maida hankali kan mutanen da ya dace waɗan da aka nufi su ci gajiyar tallafin farfaɗowa, Farouq ta ɗauki sunayen Deleget ɗin APC a matsayin waɗan da zasu amfana da kuɗaɗen.
Legit.ng Hausa ta rahoto cewa Tuni Ministar ta yi watsi da zargin wanda ta kira da yunkurin ɓata mata suna da ɓata aikin ofishinta.
Sai dai a wurin taron, Abubakar yabsake yin watsi da zarge-zargen, inda ya ce bau ɗamu ba kuma lamarin ba zai ɗauke masa hankali daga burinsa na ƙara inganta rayuwar mutane ba.
A wani labarin kuma Tsohon Ɗan majalisar tarayya daga Kano ya ce sakamakon zaɓen 2023 zai gigita yan Najeriya
Tsohon ɗan majalisa kuma mai magana da yawun Kanfen din NNPP ya ce sakamakon zaɓen 2023 zai kiɗima yan Najeriya.
Abdulmumini Jibrin ya ce babu jam'iyyar da zata samu kuri'u a jihar Kano, baki ɗaya na Sanata Rabiu Kwankwaso ne.
Asali: Legit.ng