Sakamakon Babban Zaɓen 2023 Zai Ba Yan Najeriya Mamaki, Jibril

Sakamakon Babban Zaɓen 2023 Zai Ba Yan Najeriya Mamaki, Jibril

  • Tsohon ɗan majalisa kuma mai magana da yawun Kanfen din NNPP ya ce sakamakon zaɓen 2023 zai kiɗima yan Najeriya
  • Abdulmumini Jibrin ya ce babu jam'iyyar da zata samu kuri'u a jihar Kano, baki ɗaya na Sanata Rabiu Kwankwaso ne
  • Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta tsayar da Kwankwaso a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023

Abuja - Mai magana yawun tawagar Kamfen ɗin jam'iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP), Abdulmumini Jibrin, ya yi ikirarin cewa sakamakon zaɓen 2023 zai gigita ƴan Najeriya

Tsohon ɗan majalisar ya faɗi haka ne yayin da yake tsokaci kan damar jam'iyyarsa na lashe zaɓen 2023 a wata hira da Channels tv cikin shirin 'Siyasa a yau'.

Babban zaɓen 2023.
Sakamakon Babban Zaɓen 2023 Zai Ba Yan Najeriya Mamaki, Jibril Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito a kalamansa ya ce,

Kara karanta wannan

Wani Lakcara a Jami'ar Arewa Ya Rasu a Haɗari Jim Kaɗan Bayan Gama Tsaron Jarabawa

"Ku rubuta ku aje, sakamakon zaɓen 2023 zai jijjiga yan Najeriya, duk abin da ke shirin faruwa nan da watanni shida ba zai wa PDP da APC daɗi ba. Jam'iyyar NNPP ce zata ci gajiyarsa."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Babu wata haɗin guiwa da NNPP ko Kwankwaso ke bukata, idan kana son mu haɗa karfi da kai a shirye muke, amma ka sani mu ke da mafi rinjayen kuri'u."
"Idan ka duba yadda muka gudanar da zabukan fidda gwanin mu bamu bar ko wace kafa da zata bamu matsala ba kamar yadda kuke gani yanzu, jam'iyyu na ta aibata junan su."

Ba Jam'iyyar da zata samu kuri'u a Kano - Jibrin

Jibrin ya ƙara da cewa jam'iyyar All Progressive Congress APC da PDP na ta fafutukar samun kaso 25% a kuri'un jihar Kano amma ba zai yuwu ba.

Kara karanta wannan

Daga karshe: NNPP ta yi magana game da yiwuwar hadewar Kwankwaso da Tinubu a 2023

"Mun ji labarin cewa APC da PDP na ta faɗi tashin yadda zasu sami kashi 25% na ƙuri'un Kano duk da sun san ba zasu ci jihar ba amma a lissafin su idan suka tsakuri nan da can zasu iya kai labari."
"Bari na faɗa muku wata magana, babu wata jam'iyya da zata sami 25% a Kano, zamu tarkata baki ɗayan su ga Kwankwaso kamar yadda na faɗa a baya da kuri'u miliyan biyar."

A wani labarin kuma Hotunan Yadda Tinubu, Shettima da Adamu Suka Fara Kulle-Kulle a Abuja

Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da Sanata Kasshim Shettima, sun yi wata ganawa ta dabaru da wasu jiga-jigan jam'iyya a Abuja.

shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, na daga cikin mahalarta taron tare da wasu mambobin kwamitin gudanarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262