Wani Malamin Jami'ar Jihar Kwara Ya Rasu Jim Kaɗan Bayan Fitowa Daga Tsaron Ɗalibai

Wani Malamin Jami'ar Jihar Kwara Ya Rasu Jim Kaɗan Bayan Fitowa Daga Tsaron Ɗalibai

  • Wani Malamin jami'ar jihar Kwara, KWASU, ya rasu a haɗarin mota awanni bayan gama tsaron ɗalibai dake jarabawa
  • Lakcaran mai suna, Idris Oladimeji Yahyah, ya rasu ranar Alhamis ya bar mahaifi, mata da kuma ƙaramar ɗiya ɗaya
  • Dalibai da abokanan aikin Mamacin sun nuna kaɗuwa da jin labarin rasuwar ta farat ɗaya

Kwara - Wani Malami a tsangayar koyar da ilimin kimiyyar siyasa a 'Political Science' a jami'ar jihar Kwara, Malete, Idris Oladimeji Yahyah, ya rigamu gidan gaskiya.

Daily Trust ta ruwaito cewa Lakcaran ya rasa rayuwarsa ne a wani haɗarin mota da ya rutsa da shi a kan titin Jebba yayin da yake hanyar zuwa Ilorin, babban birnin Kwara.

Idris Oladimeji Yahyah.
Wani Malamin Jami'ar Jihar Kwara Ya Rasu Jim Kaɗan Bayan Fitowa Daga Tsaron Ɗalibai Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Rahoto ya nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis, awanni kaɗan bayan Marigayin ya kammala kula da ɗalibai da ke rubuta jarabawa da jami'ar ke gudanarwa na karshen zango na biyu.

Kara karanta wannan

Wata Matashiya Da Ta Haihu Da Saurayinta Ta Sayar Da Jaririn Ɗan Mako Uku N600,000

Yadda mutane suka ji rasuwar

Ɗalibai da abokanan aikinsa sun kaɗu da jin labarin mutuwar Malamin ta farat ɗaya wacce ta karaɗe kafafen sada zumunta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan hulɗa da jama'a na jami'ar da ake wa laƙabi da KWASU a takaice, Mrs Saeedat Aliyu, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ƙara da cewa nan ba da jima wa ba zata fitar da sanarwa a hukumance.

Marigayin Malamin jami'a, ɗan asalin ƙauyen Adifa a birnin Ilorin, babban birnin Kwara ya rasu ya bar mahaifinsa, mata da kuma ɗiyarsa yar ƙarama.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Mamayi Sojoji, Sun Buɗe Musu Wuta a Jihar Zamfara

Yan bindiga sun yi wa ayarin sojoji kwantan ɓauna, an yi kazamar musayar wuta a yankin ƙaramar hukumar Bungudu, jihar Zamfara.

Mazauna yankin da abun ya faru sun ce dakarun sun maida martani kuma sun kashe dandazon yan bindigan nan take.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Raba Wa Dubbannin Mutane Tallafin N20,000 Kowanen Su a Jihar Arewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel