Zaben Fidda 'Dan Takarar Shugaban Kasa a APC: Mun Kashe N120m a Yada Labarai, Mun Dawo da N20m, Gwamna Sule
- Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya mayarwa da jam'iyyar APC canjin N20 miliyan na ragowar kudin da suka kashe a fannin yada labaran gangamin jam'iyyar
- Gwamnan kamar yadda ya bayyana, a matsayinsa na shugaban kwamitin yada labarai a zaben fidda gwanin 'dan takara shugabancin kasa, an basu N140 miliyan
- Ya mika rahoton yadda suka kashe N120 miliyan inda Sanata Abdullahi Adamu ya yaba tare da jinjinawa kwamitin yada labaran kan gaskiyarsu
FCT, Abuja - Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule a ranar Juma'a ya mika rahoton kwamitin yada labarai na zaben fidda 'dan takarar shugabancin kasa na APC da aka yi a watan Yuni.
A zaben fidda gwanin da aka yi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne yayi nasarar karbe tikitin takarar shugabancin kasa a zaben 2023 da za a yi.
A yayin mika rahoton ga shugaban jam'iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu a sakateriyar jam'iyyar na kasa a Abuja, Gwamna Sule wanda ya shugabanci kwamitin yada labarai yace an bashi N140 miliyan amma ya kashe N120 miliyan kuma ya dawo da N20m miliyan ga jam'iyyar, Daily Trust ta rahoto..
Sule yace:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Ina tunanin bayanin farko na rahoton shine bayyana godiya ga shugaban jam'iyya da NWC kan yadda suka yarda da mu, suka hada mu wurin wayar da kai a kan daya daga cikin gangami mafi inganci da aka taba yi a kasar nan.
"Kwamitin an hada shi da mutane 56. Za ka iya tunanin duk wani hazikin a fannin yada labarai a kasar nan sa aka saka a kwamitin nan," yace.
Nawa suka kashe?
A bangaren nawa kwamitin ya kashe, Sule yace:
"Da farko a ba mu N30 miliyan washegarin da aka rantsar da mu. Daga nan mun samu N60 miliyan.
"A takaice, jam'iyyar ta bamu N140 miliyan wanda muka kashe a talla, yada labarai, wurin kwana, kaiwa da kawowar wasu jami'an yada labarai dake wajen Abuja da sauransu. Bayanin yana kunshe a rahoton.
"Ga ni nan dauke da N20 miliyan wanda zan gabatarwa da shugaban jam'iyya matsayin canjin da bamu yi amfani da shi ba."
Shugaban jam'iyyar APC na kasa yace:
"Komai da zasu yi a bayyana yake ta yadda har suka kawo canji. Wasu sun kawo rahotonsu kafin yau kuma na bayyana musu cewa kun kasance misali abun koyi.
"Na farko dai kalubalenku suna da yawa amma duk da haka kun yi kokarin rage tarzomar sannan muka samu taro mai kyau."
DMO: Zunzurutun Bashin da Ake Bin Najeriya Ya Zarta Kudin Shiga da Take Samu
A wani labari na daban, Najeriya ta kashe kudade masu yawa wurin biyan bashi fiye da wanda take samu tsakanin watan Janairu zuwa Afirilu na wannan shekarar inda darakta janar na Ofishin Kula da Basusska, Patience Oniha.
Yanzu-Yanzu: Kwankwaso Ya Yi Martani Kan Rufe Ofishin NNPP Da Yan Sanda Suka Yi A Borno Gabanin Ziyararsa
Yawan kudin da ake amfani da shi wurin biyan bashi ya zama abun damuwa ga gwamnatin tarayya saboda a watanni hudu na farkon shekarar nan ta biya bashi da sama da kudin shigar da take samu.
Darakta janar din ta kara da cewa, yawan kudaden da ake biyan bashi ya karu da kashi 109 tsakanin watan Disamban shekarar da ta gabata da na Maris din wannan shekarar, daga N429 biliyan da N896 biliyan.
Asali: Legit.ng