2023: Ainihin Sababin Rikicin Wike Da Atiku, Jigon Jam'iyyar PDP Ya Yi Bayani

2023: Ainihin Sababin Rikicin Wike Da Atiku, Jigon Jam'iyyar PDP Ya Yi Bayani

  • An bayyana wasu muhimman bayanai dangane da sababin rikicin Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike
  • Tsohon shugaban PDP kuma mamba na BoT, Dakta Haliru Bello, nuna halin ko in kula da PDP ke yi wurin tattaunawa da juna ya janyo rikicin
  • Ya ce ba a sanar da Gwamna Wike ta hanyar da ya dace ba kan zaben Ifeanyi Okowa a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar

FCT Abuja - Dakta Haliru Bello, tsohon shugaban jam'iyyar PDP ya bayyana ainihin sababin rikicin da ke tsakanin Atiku Abubakar (dan takarar shugaban kasa na PDP) da Gwamna Nyesome Wike, ThisDay ta rahoto.

Bello, wanda ya yi magana a shirin siyasa na Channels Television ya ce babu bukatar a shiga damuwa kan rikicin domin tuni an cimma matsaya na warware lamarin.

Kara karanta wannan

Fidda 'Dan Takarar Shugaban Kasa a APC: Mun Kashe N120m Wurin Yada Labarai, N20m Muka Dawo da, Gwamna Sule

Atiku da Wike.
2023: Ainihin Sababin Rikicin Wike Da Atiku, Jigon Jam'iyyar PDP Ya Yi Bayani. Hoto: Leadership.
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jigon na PDP ya ce kuskuren kawai da jam'iyyar ta yi a rikicin na Wike da Atiku shine rashin yi wa gwamnan na Rivers bayani yadda ya kamata kan abin da ya faru har aka zabi Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa.

Bello ya ce:

"Na yi imanin yadda aka tafiyar da lamarin kafin sanarwar shine matsalar, kuma mutane suna da daman nuna rashin jin dadinsu kan matsalar. Wike bai yi laifi ba don ya nuna bacin rai saboda ya yi tunanin shi za a zaba, kuma lokacin da aka yanke shawarar, ba a sanar da shi ba kafin a sanarwa duniya. Ina ganin wannan shine kuskuren."

Rikicin PDP mai wucewa ne - Bello

Amma, Bello ya bada tabbacin cewa nan bada dadewa ba za a warware matsalar domin an kai matakin yin sulhu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bayan Ganawar Wike Da Tinubu, Atiku Ya Nufi Landan Don Shawo Kan Gwamnan Na Rivers

Bello, ya kuma jinjinawa Gwamna Wike a yayin da ya bayyana shi a matsayin mutum mai biyayya ga jam'iyya.

Ya ce:

"Wike mutum ne mai biyayya ga jam'iyya, ya dade yana goyon bayan jam'iyar kuma yana son ta ci zaben shugaban kasa. Bayan an tuntube shi, ina tunanin zai goyi bayan takarar Atiku Abubakar, kuma zai yi aiki don ganin PDP ta ci zaben shugaban kasa. Ina da tabbacin za a warware komai bayan wannan taron na Port Harcourt."

Wike: Sule Lamido Da Abokansa Ne Suka Kayar Da PDP A Zaben 2015

A bangare guda, gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike ya yi shagube ga tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, yana mai cewa ba shi da wata tasiri a siyasar yanzu, The Punch ta rahoto.

Lamido yayin da ya ke magana a shirin Politics Today na Channels Television a daren ranar Talata ya ce babu bukatar yin sulhu tsakanin Wike da Atiku Abubakar domin babu wanda ya yi wa gwamnan na Rivers laifi.

Kara karanta wannan

Wike: Sule Lamido Da Abokansa Ne Suka Kayar Da PDP A Zaben 2015

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164