Abin Da Muka Tattauna Da Obasanjo, Dan Takarar Shugaban Kasa Na AP
- Farfesa Christopher Imumolen, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Accord Party, ya bayyana abin da ya kai shi wurin Cif Olusegun Obasanjo
- Dan takarar shugaban kasar ya ce ya ziyarci Obasanjo ne domin neman shawarwari da albarka daga tsohon shugaban kasar da ya ce kwararre ne a bangaren mulki
- Farfesa Imumolen ya ce aikin jagorancin Najeriya ba na rago bane don haka dole duk mai neman takarar ya jajirce wurin tuntuba da shawarwari daga kwararru
Abeokuta - Dan takarar shugaban kasa na Accord Party, AP, Farfesa Christopher Imumolen ya bayyana abin da suka tattauna da tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Vanguard ta rahoto cewa ba wannan bane karo na farko da mai fatan zama shugaban kasar ya ziyarci tsohon shugaban kasar.
Yayin ziyarar, hotuna sun nuna farfesan ya rusuna kan gwiwansa yayin da Obasanjo ke masa addu'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma gabatarwa tsohon shugaban kasar da wani lambar yabo mai dauka da rubutu da ke cewa 'hidimar da jaruman mu na baya - suka yi ba zai zama asara ba' kamar yadd The Punch ta rahoto.
Abinda ya wakana tsakani na da Obasanjo, Farfesa Imumolen
Da ya ke magana kan abin da suka tattauna da Obasanjo, Farfesa Imumolen ya ce:
"Yana da kyau a samu addu'a da shawara daga manyan shugabanni irin Obasanjo wanda kwarewarsa a bangaren shugabanci ba za ta misaltu ba.
"Irin wannan addu'a da shawarwari ba za su taba min yawa ba a yayin da na ke shirin yin garambawul da tsarin shugabancin kasar nan tare da inganta tattalin arziki don kawo cigaba a Najeriya.
"Gabatar da lamban yabbon godiya ce bisa sadaukarwa da shugabancin da suka yi tsawon lokaci. Ina tuntuba don shirin jagorancin Najeriya a matsayin shugaban kasa daga 2023, sanin cewa aikin ba na rago bane.
"Ni ne zan kawo cigaban da matasan Najeriya suka dade suna neman, don haka ina rokon hadin kan yan Najeriya don ganin mun cimma wannan burin kafa gwamnatin kowa da kowa don hadin kan kasa da cigaba."
Obasanjo: A Duba Kwakwalwar Duk Wanda Ya Ce Abubuwa Na Tafiya Dai-Dai A Najeriya
A wani rahoton, Olusegun Obasanjo ya ce har yanzu Najeriya bata kai matsayin da ya kamata a ce ta kai ba.
A cewar Obasanjo, duk wanda ya ce abubuwa suna tafiya dai dai a kasar na bukatan a duba kwakwalwarsa, The Cable ta rahoto.
Obasanjo ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba wurin lakca na shekara-shekara ta Gidauniyar Badejo a Legas.
Asali: Legit.ng