Yan Majalisu Biyu Da Dubbanin Mambobi Sun Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP a Benuwai
- Jam'iyyar APC ta yi babban rashi a jihar Benuwai, yan majalisun jiha guda biyu da magoya bayan su sun koma PDP
- Gwamna Samuel Ortom ya yaba musu tare da tabbatar musu da cewa sun zo gida inda ba za'a nuna musu banbanci ba
- Jam'iyyar PDP ta samu karin goyon baya ne duk da dambarwar da ke faruwa tsakanin Atiku da gwamna Wike
Bunue - Mambobin majalisar dokokin jihar Benuwai guda biyu sun sauya sheƙa daga jam'iyyar APC zuwa PDP tare da dubbannin magoya bayan su, kamar yadda Vanguard da ruwaito.
Yan majalisun da suka sauya sheƙa sune; Thomas Kwagh-Kudi, mai wakiltar mazaɓar Makurɗi ta arewa da, Jacob Orban mai wakiltar mazaɓar Katsina-Ala ta yamma.
Gwamna Samuel Ortom da kansa ya tarbi ɗan majalisar Makurɗi a Filin Firamare Saint Mary’s Primary School da ke yankin North Bank a Makurɗi, babban birnin jihar Benuwai tare da wasu jiga-jigan PDP.
Da yake jawabi ga dandazon mutanen da suka halarci taron, Gwamna Ortom ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Jam'iyyar PDP zata cigaba da zama da karfi a jihar Benuwai, kuma zata cigaba da amsa sunanta na jam'iyyar al'umma."
Yayin da yake tabbatarwa jagoran masu sauya shekan, Mista Thomas Kwagh-Kudi da sauran yan tawagarsa cewa an zama ɗaya babu banbanci, gwamnan ya roki mutane su, "Cigaba da yin amanna da PDP sabida ita ce zata ceto Najeriya daga APC."
A nashi ɓangaren, jagoran masu sauya shekan, Kwagh-Kudi, wanda ya nuna jin daɗinsa da shiga PDP, ya ce zai yi duk me yuwuwa don ganin jam'iyyar ta yi nasara a dukkan zaɓuka.
Kun yanke hukuncin da ya dace - Ortom
A ɗaya bangaren kuma, yayin karban Mista Orban mai wakiltar mazaɓar Katsina-Ala ta yamma da magoya bayansa, gwamna Ortom ya ce tsoffin mambobin APC sun ɗauki matakin da ya dace, "Na ficewa daga jam'iyyar da ta ba yan Najeriya kunya."
Rikicin Atiku Da Wike: PDP Za Ta Rasa Mambobi Da Dama A Yayin Da Jerry Gana Yayi Barazanar Fita Daga Jam'iyyar
Tun da farko, ɗan majalisar da ya sauya shekan ya ce ya yanke fita daga APC da komawa PDP ne saboda ya samu damar haɗa karfi da gwamna domin samar da cigaba ga mutanen mazaɓarsa.
Ya ƙara da cewa jihar Benuwai ta PDP ce saboda haka ba yadda za'ai ya cigaba da zama a jam'iyyar da mutane suka tsana a yanzu.
A wani labarin kuma Sanata, Yan Majalisun Jiha da Jiga-Jigan PDP Sama da 500 Sun Fice Daga Jam'iyyar
Jam'iyyar YPP reshen jihar Akwa Ibom ta bayyana ɗaruruwan shugabanni da jiga-jigan PDP da suka koma cikinta zuwa yanzu.
Shugaban kwamitin tattara bayanan masu sauya sheƙa, Usenobong Akpabio, ya ce YPP ta kama hanyar nasara a zaɓen 2023.
Asali: Legit.ng