Aƙalla Mutum Shida Sun Mutu a Yayin Ziyarar Kwankwaso a Nasarawa

Aƙalla Mutum Shida Sun Mutu a Yayin Ziyarar Kwankwaso a Nasarawa

  • Akalla magoya bayaan Jam'iyyar NNPP Shida ne suka rasa rayukansu yayin ziyarar, Sanata Rabiu Kwankwaso a Nasarawa
  • Ɗan takarar shugaban ƙasan ya kai ziyara jihar ne domin kaddamar da sabuwar Sakatariyar NNPP a Lafiya, babban birnin jihar
  • Yayin ziyarar, Kwankwaso ya yi alƙawarin magance matsalar tsaro idan ya zama shugaban ƙasa a 2023

Nasarawa - Aƙalla Mutum Shida suka rasa rayukan su a jihar Nasarawa ranar Asabar yayin da ɗan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kai ziyara jihar.

Kwankwaso ya shiga Nasarawa ne domin kaddamar da sabuwar sakatariyar NNPP a Lafiya, babban birnin jihar, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Lamarin ya auku ne lokacin da wata Motar Bas ɗauke da magoya bayan jam'iyyar NNPP ta gagari Direban a cikin ayarin motocin ɗan takarar shugaban ƙasan, lokacin da suka shiga cikin garin Lafiya.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Sake Kai Kazamin Hari Garuruwa Takwas a Jiha Arewa, Rayuka Sun Salwanta

Kwankwaso a Nasarawa.
Aƙalla Mutum Shida Sun Mutu a Yayin Ziyarar Kwankwaso a Nasarawa Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Da yawan mutanen da ke cikin Motar sun ji raunuka kala daban-daban kuma cikin gaggawa aka kai su Asibiti domin kula da lafiyarsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Huɗu daga cikin waɗan da haɗarin ya rutsa da su sun rasu nan take a wurin yayin da wasu biyu suka ce ga garin ku nan a Asibiti.

Ɗan takarar shugaban ƙasan ya yi ta'aziyya ga iyalan Mamatan, ɗaukacin mutanen Nasarawa, da jam'iyya mai kayan marmari kan lamarin mara daɗi.

Zan magance matsalar tsaro - Kwankwaso

Kwankwaso, yayin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki da sauran mambobin NNPP, ya yi alƙawarin magance matsalar tsaro idan aka zaɓe shi shugaban kasa a 2023.

Tsohon Gwsmnan Kano ya ce idan yan Najeriya suka sahale masa ya ɗare shugaban ƙasa a 2023, zai maida hankali ya yi aiki ba dare ba rana wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Shugaban APC Na Jiha Ɗaya Ya Rasa Muƙaminsa, An Kore Shi Daga Jam'iyyar

"Mu a NNPP mun shirya samar da kyakkyawan jagoranci ga yan Najeriya, dawo da zaman lafiya, magance ƙalubalen tsaro, haɓaka tattalin arziki. Yan Najeriya sun sha baƙar wahala don haka mun zo ceto ne."

- Kwankwaso

Rabiu Musa Kwankwaso ya kuma kai ziyara fadar mai martaba Sarkin Keffi, Dr Shehu Chindo Ysmusa 111, inda ya bayyana cewa ya ziyarci Uban Ƙasa ne domin neman albarkarsa.

A wani labarin kuma Sanata, Yan Majalisu da jiga-jigan jam'iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa YPP a jihar Akwa Ibom

Jam'iyyar YPP reshen jihar Akwa Ibom ta bayyana ɗaruruwan shugabanni da jiga-jigan PDP da suka koma cikinta zuwa yanzu.

Shugaban kwamitin tattara bayanan masu sauya sheƙa, Usenobong Akpabio, ya ce YPP ta kama hanyar nasara a zaɓen 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262