Zamu Samawa Tinubu/Shettima Kuri'u 1.5M, Yan Arewa Mazauna Legas

Zamu Samawa Tinubu/Shettima Kuri'u 1.5M, Yan Arewa Mazauna Legas

  • Jama'ar Arewa mazauna Legas sun bayyana niyyar tarawa Tinubu kuri’u miliyan 1.5 a zaben 2023
  • Yan Arewan sun ce ba zasu kasa a gwiwa ba wajen baiwa Bola Ahmed Tinubu kuri'un da suka wuce wanda suka ba Fashola
  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC

Jihar Legas - Mutan Arewa mazauna jihar Legas sun bayyana niyyar baiwa Asiwaju Bola Tinubu kuri’u miliyan 1.5 a zaben shugaban kasa na 2023 mai zuwa, rahoton The Nation

Wannan ya bayyana ne yayin wani taron kaddamar da Alhaji Sa’adu Gulma, matsayin shugaban jam’iyyar APC na al’ummar Arewa dake tashar Tirela na Oko-Oba Abattoir.

Sa’adu ya ce zabensa matsayin shugaban al’ummmar Arewa na jihar Legas zai bude kofar alheri ga yan Arewa a jihar sosai.

Kara karanta wannan

Tinubu da APC Za Su San Matsayar Takararsu, Kotu Ta Sa Ranar Fara Shari’a

Ya ce kudirinsa shine tabbatar da al’ummar Arewa sun samarwa Tinubu kuri’u miliyan 1.5 a zabe mai zuwa.

Arewa
Arewa Tana Harin samarwa Bola Tinubu Kuri’u Miliyan 1.5m FOTO Sunrise News
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugabar mata Hajia Fatima Bako, ta jaddada amfanin mata shiga fagen siyasa, inda ta ce lokaci ya yi da za a biya Asiwaju da kuri’u bisa irin alheran da ya yake yiwa mutane ba tare da la’akari daga inda suka fito ba musamman bambancin addini ko yare kamar yadda Sunrise News ta rawaito.

Wata tsohuwar shugabar mata Hajiya Azabe ta tabbatar da cewa yan Arewa za su ba da kuri’u domin tabbatar da Asiwaju ya lashe zaben.

Al’umomin Arewa da suka halarci taron sun hada da mutanen jihohin Sokoto, Kebbi, kungiyar dilolin shanu, kungiyar cigaban Kabilar Shuwa Arab, da kungiyar yan Okada na yankin Arewa da sauransu.

Buratai ya Maka Sowore Kotu, Yayin Da Ya Nemi Diyyar Biliyan N10bn Dan Bata Sunan Shi

Kara karanta wannan

Rigimar Gidan PDP Ta Cabe da Fitowar Tsohon Bidiyon Shugaban Jam’iyya

A Wani labari kuma, Tsohon hafsan sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya maka mawallafin jaridar Saharar Reporters Omoyele Sowore a gaban wata babbar kotun tarayya dake birnin tarayya bisa zargin buga labaran karya akan shi. Rahoton LEADERSHIP

Buratai na neman diyyar Naira biliyan 10 ne saboda a cewarsa, Sowore, mawallafin jaridar Sahara Reporters, ta yanar gizo da ke Amurka, ya alakanta shi da wani rahoto da ke cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ICPC, ta gano biliyoyin kudade na gida da na kasashen waje a wani gida sa dake Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida