Gwamnati Zata Iya Cigaba Da Ciwo Bashi Har Karshen Duniya - Adamu

Gwamnati Zata Iya Cigaba Da Ciwo Bashi Har Karshen Duniya - Adamu

  • Shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Abdullahi Adamu, ya ce gwamnati tarayya zata iya ciwo bashi da yau har abada
  • Abdullahi Adamu ya ce muddin za anyi amfani da kudin bashi akan ayyukan da suka dace bashi da matsala da ciwo bashi
  • Adamu yace manyan kasashe duniya kamar Amurka, Canada, Faransa da Kasar Burtaniya suna rance daga cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya don biyan bukatunsu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Abdullahi Adamu, ya ce gwamnati tarayya zata iya ciwo bashi daga nan har abada. Rahoton The Cable

Abdullahi Adamu ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wata hira da yayi da gidan Talabijin na Trust TV a Ranar Alhamis.

Jagoran jam’iyyar APC yace manyan kasashe kamar Amurka, Canada, Faransa da Kasar Burtaniya suna rance daga cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya don biyan bukatunsu.

Kara karanta wannan

Kaico: Dan takarar shugaban kasa ya soki su Buhari saboda gaza gyara wutar lantarki

Adamu
Gwamnati Zata Iya Cigaba Da Ciwo Bashi Har Karshen Duniya - Adamu FOTO Legit.NG
Asali: UGC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sha suka kan yadda gwamnatin sa ke karbar bashi domin gudanar da ayyuka a fadin kasar nan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abdullahi yace bashi da matsala da ciwo bashi da kowani gwamnati zata yi, hasali ma gwamanti zata iya ciyo bashi daganan har abada idan har zata yi abun da ya kamata dasu.

Tsohon senatan yace inda yake da matsala da bashi shine wajen amfani d su a hanyar da basu dace ba.

Yanzu-yanzu : Sojoji Sun Sake Kashe Yanta’adda Da Dama A Jihar Kaduna

A wani labari kuma, Dakarun sojojin Operation Sanity sun kara kashe wasu yan bidiga a wata arrangama da sukayi a dajin gulbe dake karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna. Rahoton Leadership

Hakan na zuwa ne bayan kwanaki uku da sojoji suka kashe wasu yan bidiga da yawa.

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan ya Fadakar da Mutane a kan Shugabannin da ba za a Zaba a 2023 ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel