Magoya bayan Peter Obi Sun Ji Zafi, Sun Kai Karar El-Rufai Wajen Kamfanin Twitter
- Nasir El-Rufai ya fito Twitter ya caccaki magoya bayan ‘Dan takaran LP a 2023, Peter Obi
- A dalilin maganar da El-Rufai ya yi, an samu wanda ya kai korafi domin a taka masa burki
- Gwamnan Kaduna ya tunawa ‘Yan ‘Obidients’ cewa dole a samu wadanda za su saba da su
Kaduna - Wasu daga cikin magoya bayan Peter Obi wadanda su ke yi wa kansu lakabi da ‘Obidients’, sun fusata da kalaman da Nasir El-Rufai ya yi.
A ranar Litinin, 15 ga watan Agusta 2022, Gwamna Nasir El-Rufai ya yi magana a shafin Twitter kan gangamin da ake shirin yi wa Peter Obi a Kaduna.
Masoyan ‘dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar hamayya ta Labor Party sun sha alwashin tara mutane miliyan biyu a kan titi domin su nuna karfinsu.
Amma Gwamnan Kaduna ya maida masu martani cewa ba za su samu wadannan mutane a zahiri ba, sai dai buyagin wofin kurum a shafin sada zumunta.
Daga yin wannan magana ‘Yan ‘Obidients’ da ke dandalin suka shiga yi wa Gwamnan raddi, ta kai wasu sun gabatar da korafi a kansa ga Twitter.
Kamar yadda ya shaida da kansa, Malam El-Rufai ya nuna wani masoyin Peter Obi mazaunin kasar Jamus ne ake zargin ya kai karar maganar da ya yi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sakon da kamfanin sadarwan ya aikowa Gwamnan ya nuna Twitter ta binciki maganar da yayi, kuma ba ta same shi da aikata abin da ya saba doka ba.
A karshe dai ba a goge wannan magana ba kamar yadda magoya bayan na Obi suka nema.
Maganar da El-Rufai ya yi
“Ido rufe ‘Yan ‘Obidients’ suka fito, za su zagi duk wanda suka saba da shi, amma ba za su yarda a saba da su ba
Kuma sun manta mutane su na da ra’ayinsu. Wani daga cikinsu a Jamus ya gagara hakura da maganar da na yi.
Ga martanin @Twitter nan a kasa. HAR YANZU DARIYA NAKE YI!”
- Nasir El-Rufai
Da wata ta soki maganar El-Rufai, sai ya nuna mata matakin da gwamnatinsa ta dauka na kare Ibo a lokacin da aka yi masu barazanar barin Arewa.
Matsalar tsaro a Kaduna
An ji labari Shehu Sani ya yi tsokaci game da kokawar da Nasir El-Rufai yake yi a kan matsalar rashin tsaro, har ya aikawa shugaban kasa takarda.
Sanata Shehu Sani yace duk sai da ya yi irin wannan maganganu a majalisa, amma Gwamnati ya yake shi, aka rika nuna yana zuzuta matsalar ne.
Asali: Legit.ng