Rikicin PDP: Bani Da Shirin Yin Murabus daga Mukamina, Shugaban Jam'iyya
- Shugaban jam'iyyar adawa PDP, Dakta Ayu, ya ce ba zai sauka daga kujerarsa ba har sai zangon mulkinsa na shekara huɗu ya kare
- Ayu na cigaba da shan matsin lamba na ya sauka daga kujerarsa saboda ɗan arewa ya lashe tikitin takarar shugaban kasa
- Tsagin gwamna Wike ya jaddada sharaɗin cewa tilas Ayu ya sauka idan ana son su goyi bayan Atiku a 2023
Abuja - Shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Sanata Iyiochia Ayu, ya ce ba shi da shirin sauka daga kan kujerarsa ko anan gaba, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Shugaban babban jam'iyyar hamayya ta ƙasa ya ce ba zai sauka daga kujerarsa ba yanzu ko nan gaba kaɗan kasancewar an zaɓe shi ya shafe shekaru hudu yana jagorantar PDP.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Sanata Ayu na shan matsin lamba na ya yi murabus saboda yarjejeniyar da aka yi gabanin zaɓen shi shugaba cewa zai aje aiki idan ɗan takarar shugaban ƙasa ya fito daga arewa.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ne ya lashe tikitin PDP na takarar shugaban kasa a zaben fidda gwani, yayin da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya mara masa baya a matsayin na biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa ake son shugaban PDP ya yi murabus?
Tun bayan zaɓen fidda ɗan takarar kujera lamba ɗaya, jam'iyyar PDP ta wayi gari da sabon rikici wanda har yanzun Atiku da Wike ke nuna wa juna yatsa.
Tsagin Gwamna Wike sun jaddada matsayar su cewa tilas Ayu ya sauka daga muƙaminsa, hakan ne babban sharaɗin da gwamnan zai goyi bayan Atiku a babban zaɓen 2023.
Amma Ayu, a wani rubutu da hadiminsa ta ɓanagaren Midiya, Simon Imobo-Tswam, ya fitar ranar Litinin, ya ce ba zai yi murabus ba, vanguard ta ruwaito.
A kalamansa ya nuna cewa, "Shugaban PDP, Dakta Iyiochia Ayu, bai yi murabus ba kuma ba shi da niyyar yin murabus. Domin share tantama, an zaɓe shi ne ya yi shekara huɗu."
A wani labarin kuma Jigon Jam'iyyar APC Kuma Shugaba, Musa Abubakar, Ya Rasu a Hanyar Kano
Shugaban ƙaramar hukumar Nafaɗa a jihar Gombe, Musa Abubakar, ya rasu a haɗarin mota yau Litinin a hanyar Kano.
Gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya, ya kaɗu da jin labarin, inda yace wannan baban rashi ne ga baki ɗaya jihar.
Asali: Legit.ng