Rikicin PDP: Wasu Gwamnonin Sun Tsoma Baki Kan Rikicin Atiku da Wike
- Gwamnonin jam'iyyar PDP sun shriya zama na musamman a jihar Adamawa da nufin ɗinke barakar jam'iyyar gabanin 2023
- Bayanai sun nuna cewa gwamnonin sun yanke shiga tsakani ne da nufin kawo karshen nuna yatsa tsakanin Wike da Atiku
- A kwanakin baya, Atiku da gwamna Wike sun cimma matsayar kafa kwamitin mutum 14 da zai sulhinta su
Abuja - Ganin yadda wutar rikici tsakanin gwamnan Ribas, Nyesom Wike, da ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ke ƙara ruruwa, gwamnonin PDP sun yanke shiga tsakani don kashe wutar.
Idan baku manta ba jaridar Vanguard ta rahoto cewa gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya ziyarci gwamna Wike a Patakwal jihar Ribas ranar Alhamis da zummar rarrashinsa.
Fintiri, wanda aka naɗa shugaban kwamitin sulhu na mutum 14, ya ce ƙarƙashinsa kwamitin zai cimma sakamakon da ake mafaraki domin jam'iyyar ta shirya gabanin zaɓen 2023.
Ya kuma ƙara da bayyana cewa yan Najeriya ba zasu yafe wa PDP ba idan ta gaza samar da shugaban ƙasa na gaba a wannan lokacin, duba da abin da ya kira halin lahaula da ƙasar ta shiga ƙarƙashin APC.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Meyasa gwamnoni suka tsoma baki?
Wata majiya mai alaƙa da taron, ta gaya wa jaridar cewa gwamnonin PDP sun shirya gana wa a jihar Adamawa cikin wannan makon domin ɗinke ɓarakar Atiku da Wike.
Da take jawabi kan lamarin, majiyar ta ce:
"Ba ns kallon lamarin da saɓani, abin da nasani akwai wani shiri tattare da gwamna Fintiri na jihar Adamawa na karɓan baƙuncin takwarorinsa na PDP a jihar."
"Ban sani ba ko sun zaɓi ranar taron amma ina da tabbacin zasu gana ne a cikin makon nan ko mako mai zuwa. Gwamnonin zasu haɗu su tattauna kan batutuwan da ake ganin zasu dunƙule PDP."
Rawar da Fintiri zai taka
A cewar majiyar, Gwamna Fintiri ne ɗan tsakiya kuma ana ganin shi ne zai iya haɗa kowane ɓangare a inuwa ɗaya domin a tattauna.
"Bani da masaniya ko gwamnonin na kus-kus a tsakanin su, kuma kunsan cewa su kan yi taronsa daga wannan jihar zuwa waccan. Fintiri bai taɓa karɓan bakuncin taron su ba, wannan lokacinsa ne."
"Wasu gwamnonin suna da yaƙinin wannan karon a Adamawa zasu haɗu, ana ganin Fintiri a matsayin ɗan tsakiya da ka iya haɗa kowane ɓangare wuri guda."
A wani labarin kuma kun ji cewa Atiku ya naɗa Gwamnan Arewa a Matsayin Shugaban kwamitin da zai rarrashi Gwamna Wike
Ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya naɗa gwamnan Adamawa a matsayin shugaban tawagar sulhu da Wike.
Ahmadu Fintiri, ya tabbatar da cewa kafin babban zaɓen 2023 komai zama tarihi a rikicin Atiku da gwamna Nyesom Wike.
Asali: Legit.ng