Barayin Fasinjan Jirgin Kasa sun Yaudari Gwamnati Bayan sSakin Iyalansu
- Fadar shugaban kasa ta ce, yan ta’adan da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasar dake jigila daga Abuja zuwa Kaduna sun yaudari gwamnati
- Shugaba Buhar ya gana da iyalan fasinjojin da yan bindiga suka yi garkuwa da su a ranar Alhamis a fadar shugaban kasa
- Garba Shehu ya ce Gwamnati ta biya bukatar Shugaban Masu Garkuwa da mutane na sakin matar sa mai juna biyu amma ya saba alkawari
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Fadar shugaban kasa ta ce, yan ta’adan da suka yi garkuwa da fasinjojin jirgin kasa dake jigila daga Abuja zuwa Kaduna sun yaudari gwamnati. Rahoton BBC
A lokacin da suke tattaunawa da gwamantin sun mata alkawarin cewa zasu sako fasinjojin jirgin kasa da suka sace idan ta biya musu bukatun su.
Hadimin Shugaban kasa a fanin yada labarai Malam Garba Shehu, ya bayyana haka inda ya shaidawa BBC cewa gwamnatin tarayya ta biya wa shugaban wanda suka yi garkuwa da fasinjoji jirgin kasa bukatarsa amma ya saba alkawari.
Garba Shehu yace Shugaban 'yan ta'addan ya nemi gwamnati ta saki matarsa mai juna biyu kuma bayan haka aka kai ta asibiti ta haifi tagwaye, aka nuna masa cewa matarsa da 'ya'yansa na cikin koshin lafiya, kuma aka mika wa iyayensa su.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Malam Garba, ya kara da cewa bayan gwamnati ta yi hakan sai yan ta’adan suka kara bijiro da sabbin bukatu.
Jawaban nan sun fito ne awanni kadan bayan Shugaban Buhari ya gana da yan uwan fasinjojin da aka sace a fadar sa a ranar Alhamis.
Shehu ya ce hakan bashi bane karon na farko da yan ta’adda ke saba alkawarin da aka yi da su ba, amma shi ne karon farko da gwamnatin ta faɗa da bakinta da kuma ainihin bukatun yanta'adan.
Har yanzu akwai fasinjoji 31 a hannun masu garkuwar a cikin daji, amma gwamantin ta ce ba za ta yi amfani da karfifi ba wajen ceto su, saboda dukan sufito a raye.
Mun Kashe Triliyan N3.2 Da Muka Kwato Daga Barayin Gwamnati — Malami
A wani labarin kuma, Abuja Babban Lauyan gwamnati kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, yace Najeriya ta kwato Naira triliyan 3.2 da aka sace daga kasar aka boye a bankuna daban-daban a duniya.Rahoton Aminiya
Abubakar Malami ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da yan jarida a Fadar shugaban kasa a ranar Alhamis
Asali: Legit.ng