Gaskiya Za ta Fito, Kotu ta sa Ranar Fara Shari’a da ‘Dan takaran APC, Bola Tinubu

Gaskiya Za ta Fito, Kotu ta sa Ranar Fara Shari’a da ‘Dan takaran APC, Bola Tinubu

  • A watan Satumba mai zuwa ne Bola Tinubu zai bayyana a kotu kan zargin yi wa hukumar karya
  • Wasu ‘Yan APC sun shigar da karar ‘dan takararsun, suna tuhumarsa da yi wa INEC karya a 1999
  • Tinubu yana ikirarin ya yi karatu a Ibadan, masu karar sun karyata shi, sun ce shaidar zir ya bada

FCT, Abuja - A ranar 7 ga watan Satumban 2022, za a shiga kotun tarayya da Bola Ahmed Tinubu a kan zargin da ake yi masa na amfani da takardun bogi.

Rahoton da muka samu daga tashar talabijin na Channels TV ya bayyana cewa za a saurari wannan kara ne a babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja.

Alkali Ahmed Mohammed ya sa ranar da za a zauna domin sauraron karar da aka gabatar masu, ana tuhumar ‘dan takaran APC a zaben shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Duk bula ce: Ainihin Abin da ya sa Ake Barazanar Sauke Buhari inji Dan Majalisa

Rahoton yace wadanda suka shigar da wannan kara wasu mutane hudu ne daga cikin jagororin APC wadanda ke nema a hana Tinubu shiga takaran 2023.

Dalilin kai Tinubu kotu

Masu karar sun fake da cewa wanda APC ta ba tutan ya ba hukumar INEC bayanan da ba gaskiya ba ne. Sai an saurari karar sannan za a san gaskiyar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan masu kara, Goddy Uche ya fadawa kotu cewa ya zama dole su kawo shari’ar zuwa teburin Alkali domin sun gagara samun ‘dan takaran shugaban kasar.

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Kashim Shettima Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Za a koma kotu a Satumba

Vanguard tace Mai shari’a Mohammed ya bukaci a sanar da Bola Tinubu da wannan kara da aka kai. Bayan nan sai ya dakatar da sauraron shari’ar sai Satumba.

A ranar 7 ga watan Satumba mai zuwa za a cigaba da zama a kotun na Abuja domin fara shari’ar gadan-gadan. Ana sa ran Tinubu zai kawo Lauya da zai kare shi.

Kara karanta wannan

An Sake Samun Lauyan da Ya Kai INEC Kara a Kotu Saboda Takarar Bola Tinubu

Daga cikin zargin da lauyan ‘dan takaran na APC zai amasa shi ne Tinubu ya yi karya da ya fito takarar gwamna a 1999 cewa yayi karatun firamarensa a Ibadan.

Haka zalika Lauyan masu kara yana zargin tsohon gwamnan da karya da ya fadawa INEC ya halarci makarantar sakandaren gwamnati na garin Ibadan a 1965.

A cewar masu karar, Tinubu bai je wadannan makarantu tsakanin 1958 da 1968 ba, don haka ne da ya tashi cike fam din takaran 2023, ya boye wannan magana.

Tsige shugaban kasa

Dazu aka ji labari 'Dan Majalisa mai wakilatar Akoko a Majalisar Wakilan Tarayya ya kawo dalilan da za su hana a tumbuke Mai girma Muhammadu Buhari.

Hon. Adejoro Adeogun wanda tun 2015 yake Majalisa yace duk wanda ya san dokar kasa, ya san babu lokacin da burin ‘Yan adawa zai tabbata kafin zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng