Atiku Ya Shirya Gangami, Zai Karbi Mambobin APC Sama Da 1,000 zuwa PDP

Atiku Ya Shirya Gangami, Zai Karbi Mambobin APC Sama Da 1,000 zuwa PDP

  • Mambobin jam'iyyar APC sama da dubu ɗaya sun sauya sheƙa zuwa babbar jam'iyyar hamayya PDP a jihar Adamawa
  • A cewar wakilan masu sauya sheƙan ba su kenan ba, sun kai mutum 6,000 da suka yanke barin APC saboda gazawar Buhari
  • A ranar 15 ga watan Agusta, Atiku zai gudanar da gangamin murna a jiharsa, ya nemi masu sauya shekar su hallara

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Adamawa - Jam'iyyar PDP ta karɓi mambobin jam'iyyar All Prigressive Congress watau APC 1,615 waɗan da suka sauya sheƙa a ƙaramar hukumar Toungo, jihar Adamawa ranar Lahadi.

Punch ta ruwaito cewa ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya shirya gaisawa hannu da hannu da su a wurin wani babban gangami da ya shirya gudanarwa ranar 15 ga watan Agusta a Yola.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Atiku Ya Shirya Gangami, Zai Karbi Mambobin APC Sama Da 1,000 zuwa PDP Hoto: punchng
Asali: Depositphotos

Shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Adamawa, Tahir Shehu, shi ne ya karɓi masu sauya shekar daga APC, waɗan da a ganin su shugaban ƙasa ya gaza.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Naɗa Tsohon Ɗan Majalisar Tarayya Daga Kano a Wani Babban Matsayi

Meyasa Suka sauya sheka?

Masu sauya shekan sun bayyana cewa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya gaza cika alƙawurran da ya ɗauka, sannan ga matsalar tsaro na ƙara tabarbarewa duk karkashin gwamnatin APC.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da suke jawabi a madaɗin masu sauya sheƙan, Mustapha Albashir, Alhaji Gana da Yahya Abubakar, sun ambaci taɓarɓarewar tsaro, talauci, matsin tattalin arziki da ƴan ƙasa ƙe fama da su karkashin Buhari a matsayin dalilin su na barin APC.

Kazalika sun nuna dana sanin su bisa rashin ganin cigaba tun 2015 da suka hana idon su bacci don ɗora APC amma yanzu sun gane gaskiyar PDP ce wacce ta dace duba da canjin da Ahmadu Fintiri ya kawo.

"Tafiyar da muka yi a APC ba ta da amfani, mun taru mun murkushe PDP a 2015 amma yanzu mun gano mun tafka babban kuskure."

Kara karanta wannan

2023: Jerin Sunayen Jihohi 20 da Jam'iyyar APC Ka Iya Shan Kaye a Zaɓe Saboda Rikici

"Wannan na ɗaya daga dalilan da suka sa mu 1,615 muka yanke dawo nan duk da cewa mun fi 6,000 da muka koma PDP saboda bamu ga komai ba a mulkin Buhari sai talauci da rashin tsaro."

Atiku na son ganin masu sauya shekar

Shehu, yayin karɓan masu sauya shekan, ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya ce zai so ya gaisa hannu da hannu da masu sauya sheka 1,615, waɗan suka fito yaƙar azzalumar gwamnati.

"Atiku ya nemi jam'iyya ta tabbatar ku 1,615 da kuka sauya sheka a Toungo kun halarci babban gangaminsa a Yola ranar 15 ga Agusta Saboda zai so yin musabaha da ku."

A wani labarin kuma Matakai 33 da Gwamnoni Suka Shawarci Buhari Ya Ɗauka Don Ceto Najeriya Daga Durkushewa

Gwamnonin Najeriya sun shawarci gwamnatin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ta ɗauki wasu matakai cikin gaggawa a wani yunkurin rage wahalhalun kasafin kuɗi da ceto ƙasa daga durkushewar tattalin arziki

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gida: Bayan Shan Kaye, Ɗan Uwan Shugaba Buhari Ya Fice Daga Jam'iyyar APC

Gwamnonin sun gabatar da matakan yayin gana wa da shugaba Buhari a watan da ya shuɗe, rahoton Premium Times ya tabbatar daga wata majiya da bat da ikom faɗin abinda aka tattauna a taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262