2023: Jerin Jihohin Najeriya 20 Da APC Ka Iya Shan Kaye Saboda Rikicin Cikin Gida
Idan har ikirarin shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, cewa rikicin cikin gida ne ya jawo musu faɗuwa a zaɓen Osun, kuma ya kasance Mai ɗorewa, APC na fuskantar faruwar irin haka a jihohi 20.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Mafi yawan rassan jam'iyyar APC na jihohi sun shiga cikin rikici sakamakon saɓani ko kuma wani abu da ya biyo bayan zaɓen fidda gwani.
Binciken da aka gudanar a dukkan sassan ƙasar nan ya nuna cewa duk da kiran da shugaban ƙasa Buhari ya yi ga mambobin APC cewa kowa ya maida wuƙar shi kube, wasu da suka fusata basu ɗauki lamarin da sauki ba.
Yayin da wasu suka ɗauki matakin sauya jam'iyya, inda wasu suka koma PDP, wssu kuma suna nan daram a APC amma zasu iya komawa gefe su yaki jam'iyyar kamar yadda ta faru a jihar Osun.
Adamu ya ce rashin fahimtar juna a cikin gida da rashin haɗin kai ne ya jawo wa jam'iyyar APC rashin nasara a zaɓen jihar Osun.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jerin Jihohin da haka ka iya faruwa da APC a 2023
Legit.ng Hausa ta haɗa muku jerin sunayen jihohin da APC ke fama da rikicin cikin gida, wanda idan abun da ya faru a Osun ya cigaba, jam'iyyar na fuskantar bazanar faɗuwa.
Jihohin sun haɗa da, Legas, Ondo, Eikiti, Ogun, Oyo, Abiya, Kano, Kaduna, Kebbi, Akwa Ibom, Ribas, Nasarawa, da jihar Benuwai.
Sauran jihohin su ne; Ebonyi, Kwara, Imo, Kuros Riba, Bauchi, Zamfara da kuma jihar Gombe.
Jam'iyyar APC na fuskantar yaƙi mai zafi yayin da babban zaɓen 2033 ke tafe. Bincike ya nuna matukar ba'a shawo kan mambobin da suka fusata ba, jam'iyyar ka iya faɗuwa a zaɓe.
A wani labarin kuma Wata Sabuwa A Rikicin PDP, Gwamna Wike Da Atiku Abubakar Sun Cimma Wata Matsaya Ɗaya
Ga dukkan alamu jam'iyyar PDP ta fara nemo bakin zaren game da rikicin ɗan takararta, Atiku Abubakar da gwamna Wike.
Wani ƙusa a jam'iyyar ya tabbatar da cewa ganawar mutanen biyu ta yi armashi har sun fara lalubo hanyar sasantawa.
Asali: Legit.ng