2023: Kar Ku Yi Tsammanin Cin Zabe A Arewa Maso Yamma, APC Ta Gayawa Jam'iyyun Adawa

2023: Kar Ku Yi Tsammanin Cin Zabe A Arewa Maso Yamma, APC Ta Gayawa Jam'iyyun Adawa

  • Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso yamma Salihu Lukman ya shawarci Jam'iyyun adawa da kada su yi tsammanin cin zabe yankin sa
  • Salihu Lukman ya ce jam’iyya APC mai mulki tana aiki tukuru don ganin ta samu nasara a zabe mai zuwa
  • Jam'iyyar APC ta ce yunkurin sasanta mambobin jam’iyyar dake fushi yana samun sakamako mai kyau

Jihar Kaduna - Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso yamma Salihu Lukman, ya bukaci jam’iyyun adawa da kada su yi tunanin samun nasara a zaben 2023. Rahton Daily Trust

Lukman ya bayyana haka ne a Kaduna a wata tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan ganawarsa da shugabannin jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Yamma.

A cewarsa, jam’iyya mai mulki tana aiki tukuru don ganin ta samu nasara a zabe mai zuwa domin shiyyar Arewa Maso Yamma ta APC ce.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Atiku ya ba da Dino Malaye babban matsayi a tawagar kamfen dinsa

APC P
2023: Kar Ku Yi Tsammanin Cin Zabe A Arewa Maso Yamma, APC Ta Gayawa Jam'iyyun Adawa FOTO Legit.NG
Asali: Facebook

Lukman ya ce yunkurin sasanta mambobin jam’iyyar dake fushi yana samun sakamako mai kyau, amma akwai bukatar a kara kaimi kafin a fara yakin neman zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce shiyyar ta kuma sake duba rahoton hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) dangane da batun rufe rajistar masu zabe.

Ya bayyana cewa jam’iyyar ta amince da kwamitocin su hada kai da mutanen da suka yi rajista domin karbar katin zabe na dindindin (PVCs).

Rundunar 'Yan sandan Najeriya Ta Sanar Da Shirin Daukar Sabbin Dalibai

A wani labari kuma, Rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF) ta gayyaci ‘yan kasa masu sha’awar shiga aikin Dansanda da su yi rajistar shiga kwalejin Karatun dansanda na digiri karo na Tara. Rahoton THE CABLE

Olumuyiwa Adejobi, jami’in hulda da jama’a na rundunar ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa