Rashin Tsaro: Za Mu Raba Lawan Da Kujeransa Idan Ya Kawo Mana Cikas Wurin Tsige Buhari, In Ji Sanatan Najeriya

Rashin Tsaro: Za Mu Raba Lawan Da Kujeransa Idan Ya Kawo Mana Cikas Wurin Tsige Buhari, In Ji Sanatan Najeriya

  • Sanata Francis Fadahunsi, mataimakin shugaban kwamitin kwastam a majalisar tarayyar Najeriya ya ce za su cire Lawan Ahmad daga kujerarsa idan ya nemi ya hana tsige Shugaba Buhari
  • A baya-bayan nan ne dai yan majalisar na dattawa suka bawa shugaban Muhammadu Buhari wa'adin makonni shida ya samar da tsaro a kasar idan ba haka ba su tsige shi
  • Fadahunsi ya ce baya tsammanin Buhari zai iya magance matsalar cikin sati shidan yana mai cewa da zarar sun dawo hutu a Satumba za su fara shirin tsige Buhari kuma duk wanda ya nemi a taka musu birki shima za su tube masa mukaminsa

Mataimakin shugaban kwamitin kwastam, Sanata Francis Fadahunsi ya ce takwarorinsa sun cimma matsaya cewa za su cire Ahmad Lawan, idan ya yi yunkurin dakile kokarin da suke yi na tsige Shugaba Muhammadu Buhari a wata mai zuwa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wani Babban Malami A Najeriya

Fadahunsi, yayin martani kan maganganun kakakin shugaban kasa ya ce shi da takwarorinsa sun gama shawarar cigaba da tsige shugaban kasar, This Day ta rahoto.

Francis Fadahunsi.
Rashin Tsaro: Za Mu Raba Lawan Da Kujeransa Idan Ya Kawo Mana Cikas Wurin Tsige Buhari, Sanata Fadahunsi. Hoto: @thisdaylive.
Asali: Twitter

Jigon na PDP wanda ke wakiltan Osun ta Gabas a majalisar ya furta hakan ne a hirar da ya yi da manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, mako daya bayan wa'adin da aka bawa Buhari.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce mafi yawan sanatoci daga dukkan jam'iyyu tuni sun jefa kuri'ar rashin gamsuwa kan Shugaba Buhari saboda gazawar gwamnatinsa wurin magance matsalar tsaro da ke damun kasar.

Ya ce baya tsammanin Buhari zai iya magance matsalar tsaro da ke fuskantar kasar cikin sati shida idan ya kasa yi cikin shekaru bakwai.

Ya sha alwashin cewa za a cigaba da shirye-shiryen tsige shugaban kasar da zarar takwarorinsa sun dawo daga hutunsu na sati shida a ranar 20 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Muna Bukatar Shirin Da Zai Sa Mu Gaba Da Yan Ta’adda – Osinbajo Ya Fadawa Sojoji

Wani sashi cikin jawabinsa:

"Mun dade muna maganganu da bada shawarwari kan yadda za a kawo karshen matsalar tsaro amma jagoran (shugaban majalisa) a manne ya ke da Villa. Ya dade yana dakile kokarin mu na daukan mataki kan shugaban kasa.
"Yanzu mun cimma matsaya ba za mu bata lokaci ba muna hada kai da Lawan a lokacin da yan ta'adda ke lalata kasar mu kuma gwamnati bata da shirin taka musu birki. Ba za mu jira sai an kashe dukkan mu ba."

Ya kara da cewa:

"Za mu tsige duk wanda ya ce ba za mu tsige Buhari ba. Duk wanda ya yi kokarin hana mu, ko shugaban majalisa ko wani daban, za mu cire mutumin," in ji shi.

Sanatocin PDP sun fice daga majalisa cikin fushi a lokacin da Lawan ya hana fara tsige Shugaba Buhari kan gazawa wurin magance matsalar tsaro.

Sanata Daga Arewa Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Baya Goyon Bayan Tsige Buhari

Kara karanta wannan

Gwmnatin Tarayya Ta Saya Wa Jamhuriyyar Niger Motocin Naira Biliyan 1.4

A wani rahoton, Shugaban kwamitin labarai da wayar da kan kasa na majalisar dattawa, Danladi Sankara ya nesanta kansa daga shirin da ake yi na tsige Shugaba Muhammadu Buhari, rahoton Daily Trust.

Sanata Sankara, wanda ke wakiltar Jigawa North West a Majalisar ya kuma nesanta kansa daga shirin tsige shugaban majalisa, Ahmad Lawan.

Sanatocin jam'iyyun adawa, a ranar Laraba, bayan tattaunawa na away biyu sun bawa Buhari wa'adin wata shida ya magance matsalar tsaro ko kuma su tsige shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164