Daga Karshe, Gwamna Wike Da Atiku Abubakar Sun Gana A Gidan Tsohon Minista a Abuja
- A karon farko tun bayan zaɓen fidda gwani, Atiku Abubakar da gwamna Wike sun gana a birnin tatayya Abuja
- Wata majiya ta ce taron ya yi armashi sosai kuma akwai wasu taruka da zasu biyo baya a kwanaki kaɗan masu zuwa
- Jam'iyyar PDP ta afka cikin rikici ne bayan zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa, wanda Wike ya sha kaye
Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, sun gana a wani yunkuri na kawo karshen rikicin PDP a babban birnin tarayya Abuja.
The Cable ta fahimci cewa taron ya gudana ne a gidan tsohon Ministan yaɗa labarai kuma mamban kwamitin amintattu BoT, Farfesa Jerry Gana.
Wata majiya ta bayyana cewa taron na yau Alhamis ya haifar ɗa mai ido kuma akwai taruka da zasu biyu baya na, "Ɗinke ɓaraka," waɗan da zasu maida hankali wajen kawo karshen saɓanin da ke faruwa a jam'iyya tun bayan zaɓen fidda gwani.
Punch ta rahoto Majiyar ta ce:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Nyesom Wike da Atiku Abubakar sun gana yau a gidan Farfesa Jerry Gana da ke Abuja, taron ya yi armashi, kuma akwai wasu tarukan da zasu biyo baya a kwanaki masu zuwa."
"Sun gaisa da juna tare da yi wa juna fatan alheri kuma sun cimma matsayar zuwa mataki na gaba a kokarin yin sulhu.
Taron ya zo ne awanni bayan kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP (BoT) ya kafa sabon kwamitin sulhu da zai kawo ƙarshen sabanin da ke tsakanin mutanen biyu.
Tun a ranar Lahadi, bayan gana wa da Wike, makusantansa da wasu gwamnonin PDP, Farfesa Gana ya ce zasu bayyana wa yan Najeriya duk halin da ake ciki idan an samu cigaba.
"Mun yi taro a karon farko bayan zaben fidda yan takarar PDP, mun sake duba abubuwan da suka shafe mu babu rufa-rufa. Muna tabbatar da cewa kan mu haɗe yake a matsayin tawaga."
A wani labarin kuma kun ji cewa BoT Sun Kafa Kwamitin Sulhu Da Zai Gana Da Wike, Fusatattun Mambobi
Mambobin BoT na jam'iyyar PDP sun yunkuro da wani babban shiri da nufin kawo karshen rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyyar.
A taron da suka gudanar yau Laraba, BoT sun kafa sabon kwamitin da suka ɗora wa alhakin rarrashin mambobi irin su Wike da suka fusata.
Asali: Legit.ng