2023: Gwamnan Adamawa Ya Zabi Farfesa Mace A Matsayin Abokiyar Takararsa

2023: Gwamnan Adamawa Ya Zabi Farfesa Mace A Matsayin Abokiyar Takararsa

  • Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya zabi Farfesa Kaletapwa Farauta a matsayin mataimakiyarsa
  • Gwamna Fintiri ya ce an zabe ta ne saboda halayenta na gaskiya da rikon amana da jajircewa da kuma tafiya tare da mata a gwamnati
  • A bangarenta, Farfesa Farauta ta mika godiya ga gwamnan bisa wannan damar da ya bata ta kuma yi alkawarin yin aiki tukuru

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa ya zabi farfesa mace, Kaletapwa Farauta, a matsayin abokiyar takararsa domin zaben shekarar 2023.

Farfesa Farauta a halin yanzu ita ce shugaban jami'ar Jihar Adamawa da ke Mubi.

Fintiri
2023: Gwamnan Adamawa Ya Zabi Farfesa Mace A Matsayin Abokiyar Takarsa. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A bikin kaddamar da ita da aka yi a Yola a ranar Laraba, Fintiri ya ce an zabi Farfesa Farauta ne saboda gaskiyarta, rikon amana da aiki tukuru.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wata Amarya Da Mahaifinta Suka Fashe Da Kuka A Wajen Liyafar Bikinta

Ya ce ana sa ran za ta yi ayyukanta cikin gaskiya da tsoron Allah, bugu da kari za ta cigaba da aikinta na gida a matsayin matar aure.

"An zabe ta ne bayan lissafi da nazari musamman bukatar dama wa tare da mata a siyasa," in ji shi.

Gwamna Fintiri ya bukaci jam'iyyun adawa ta hada kai da gwamnatinsa wurin aiki don cigaba da inganta jihar.

Jawabin Farfesa Farauta

A jawabinta, Mrs Farauta, wacce ta bayyana zabinta a matsayin ikon Allah, ta mika godiya ga Mr Fintiri da jam'iyyar PDP saboda damar da aka bata.

Ta bada tabbacin cewa za ta yi aiki tukuru da biyayya da tsoron Allah ta kuma ce:

"Za mu yi aiki tukuru don tabbatar da nasarar jam'iyyar mu a zaben da ke tafe."

An haifi Mrs Farauta ne a ranar 28 a shekarar 1965 a karamar hukumar Numan a jihar Adamawa, ita ce kuma mace ta farko da ta fara zama shugaban jami'a a Arewa maso Gabas a Jami'ar Jihar Adamawa a Mubi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164