Garabasa: Matashi ya bude shagon aski, yana aski kyauta saboda kaunar Peter Obi

Garabasa: Matashi ya bude shagon aski, yana aski kyauta saboda kaunar Peter Obi

  • Masoya Peter Obi na ci gaba da zage damtse wajen nuna kauna da goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Labour
  • Wani matashi a jihar Gombe ya ba da nasa gudunmawa ta hanyar yi wa jama'a aski kyauta a yankinsu
  • Magoya bayan jam’iyyar Labour sun yaba wa matashin da ba a tantance sunansa ba saboda sha’awar da ya nuna na goyon bayan Obi

Billiri, jihar Gombe - Wani matashi mai sana'ar aski a jihar Gombe ya fara yiwa mazauna yankinsu hidimar aski kyauta domin nuna goyan baya ga yakin neman zaben shugabancin kasa na Peter Obi.

Hotunan matashin da ke aski kyauta ga matasan da suka yi layi a gaban shagonsa ya bazu a shafukan sada zumunta.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Wata Amarya Da Mahaifinta Suka Fashe Da Kuka A Wajen Liyafar Bikinta

A baya dai ya gayyaci mutane zuwa wajen kaddamar da shagon a wani rubutu da ya wallafa a ranar Asabar, 30 ga watan Yuli.

Matashi mai aski kyauta a jihar Gombe
Garabasa: Matashi ya bude shagon aski, yana aski kyauta saboda Peter Obi | Hoto: correctng.com
Asali: UGC

A rubutun ya bayyana cewa, shagon zai yiwa jama'a aski kyauta saboda ba da gudunmawa ga nasarar Peter Obi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, shagon yana nan a yankin Billiri ta Gabas, a jihar Gombe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Hakazalika, ya ce tsofaffi da yara kana ya su kwal kobo da dai sauran nau'in aski na zamani, ciki har da wankin kai da man gashi duk dai kyauta.

Tuni mutanen yankin Arewa maso Gabas da ke goyon bayan Peter Obi suka fara yada rubutun dauke da hotunan yadda matashin ya dauki nauyin wannan tafiya.

Kalli hotunan anan:

Daga Rubutu a Kan Peter Obi, Magoya-baya na Barazanar Kashe Ni inji Marubuci

Kara karanta wannan

El-Rufai: Na Fadawa Tinubu Ban Bukatar Komai a Gwamnatinsa, Na Bada Dalilina

A wani labarin, shahararren ‘dan jaridar kasar nan, Sam Omatseye, ya koka game da barazanar da yake fuskanta a dalilin wani rubutu da yayi a makon jiya.

Legit.ng Hausa ta fahimci Sam Omatseye ya tada kura musamman a shafukan sada zumunta tun bayan rubutun da ya yi wanda ya yi wa take da ‘Obi-tuary’.

Omatseye ya fito shafinsa na Twitter yana mai cewa magoya bayan ‘dan takarar jam’iyyar Labor Party, Peter Obi suna yi masa barazana har ga rayuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.