Addini Ba Zai Hana Kiristocin Arewa Zaben Tikitin Musulmi da Musulmi ba

Addini Ba Zai Hana Kiristocin Arewa Zaben Tikitin Musulmi da Musulmi ba

  • Darakta Janar na Hukumar Muryar Najeriya VON ya yiwa yan Najeriya jawabi kan muhimmancin cancanta kan addini ko kabilanci a zaben 2023
  • Osita Okechukwu ya ce dan takarar jam’iyyar APC yana da basira da kwarewar tunkarar kalubalen da ke gaban shi na shugabanci Najeriya
  • Osita ya ja hankalin ‘yan Najeriya da su ajiye addini da kabilanci a gefe wajen kada kuri’a, su zabi cancanta

Darakta Janar na Hukumar Muryar Najeriya VON, Osita Okechukwu, ya yi wa ‘yan Najeriya jawabi kan muhimmancin cancanta kan addini ko kabilanci a zaben 2023. Rahoton Arise News

Osita Okechukwu,ya bayyana cewa dan takarar jam’iyyar APC yana da basira da kwarewar tunkarar kalubalen da ke gaban shi na shugabanci Najeriya.

Osita Ya bayyana haka ne a wata hira da yayi a safiyar ranar Talata a gidan Talabajin Din Arise TV mai taken "The Morning Show" inda ya ce:

Kara karanta wannan

Buhari Ya Jajantawa Rundunar Yansanda Da Mutanen Jihar Osun Kan Rasuwar Tafa Balogun

"Basirar da nake dashi akan harkar siyasa yasa na san kristocin Arewa za su goyi bayan Tikitin Musulmi da Musulmi a zaben 2023 mai zuwa duk da matsayin na kirista na so Tinubu ya dauki abokin takara kirista
Osita
Addini Ba Zai Hana Kiristocin Arewa Zaben Tikitin Musulmi da Musulmi ba – Osita Okechukwu
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ku tuna cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shetttima, dan sa uwa musulmi, a matsayin abokin takararsa wanda ya janyo cece-ku-ce a tsakanin mabiya addinin Kirista a Najeriya, wadanda suke ganin an mayar da su koma baya sabdoa tikitin musulmi da musulmi.

Hakan dai ya fito ne sakamakon kin amincewa da tikitin da kungiyar kiristoci ta Najeriya tayi.

Dangane da wannan takaddama, Okechukwu ya dage kan cewa tikitin Musulmi da Musulmi na jam’iyyar APC shi ne mafi kyawu wajen fitar da ingantacciyar shugabanci da ake hasashen za a yi a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Atiku ya ba da Dino Malaye babban matsayi a tawagar kamfen dinsa

Ya kuma ja hankalin ‘yan Najeriya da su ajiye addini da kabilanci a gefe wajen kada kuri’a su zabi cacanta, bayan haka su maida hankali wajen ciyar da kasar gaba.

An Riga An Zabi Darakta Janar Na Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa A APC, Inji El-Rufai

A wani labari kuma, Gabanin zaben 2023, an zabi babban darakta a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC). Rahoton Channels TV

Wannan shine jawabin gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ya bayyanawa manema labarai a ranar Litinin bayan ganawar da gwamnonin APC suka yi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Bola Tinubu, da abokin takararsa Kashim Shettima, a Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa