Sanata Daga Arewa Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Baya Goyon Bayan Tsige Buhari
- Sanata Danladi Sankara daga Jihar Jigawa ya bayyana cewa baya goyon bayan sanatoci da ke son tsige Shugaba Muhammadu Buhari
- Sankara ya ce babu wanda ya tuntube shi kan batun kuma babu wanda ya nemi izininsa kuma ya ce baya cikin wadanda ke son tsige shugaban majalisa Ahmad Lawan
- A cewar shugaban na kwamitin watsa labarai da wayar da kan kasa na majalisa, dattaku da fahimta da goyon baya ga shugabanni ake bukata don magance matsalar ba dumama siyasa ba
Shugaban kwamitin labarai da wayar da kan kasa na majalisar dattawa, Danladi Sankara ya nesanta kansa daga shirin da ake yi na tsige Shugaba Muhammadu Buhari, rahoton Daily Trust.
Sanata Sankara, wanda ke wakiltar Jigawa North West a Majalisar ya kuma nesanta kansa daga shirin tsige shugaban majalisa, Ahmad Lawan.
Sanatocin jam'iyyun adawa, a ranar Laraba, bayan tattaunawa na away biyu sun bawa Buhari wa'adin wata shida ya magance matsalar tsaro ko kuma su tsige shi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sanatocin da farko sun yi fushi sun fita daga zauren Majalisar suna rera waƙar cewa "Buhari must go" ma'ana dole Buhari ya tafi a lokacin da Shugaban majalisar ya ki yarda a tattauna kan batun tsige shugaban kasar.
Batun tsige shugaban kasar ya samu tagomashi a ranar Laraba a lokacin da mambobin PDP a majalisar wakilai suka hada kai da takwarorinsu a majalisar dattawa.
Matakin na yan majalisar na zuwa ne a lokacin da hare-hare ke yawaita a birnin tarayya Abuja.
Sanata Sankara, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar ya ce babu wani lokaci da aka tuntubi shi ko ya goyi bayan shirin tsigewar.
"Na hallarci zaman majalisar a ranar Talata da Laraba, babu wanda ya tuntube ni ko ya nemi izini na don goyon bayan tsige Shugaba Muhammadu Buhari ko shugaban majalisa," in shi.
Abin da yasa bana goyon bayan tsige Buhari, Sanata Sankara
A cewarsa, abin da ke da muhimmanci shine a wannan lokacin fahimta da dattaku na shugabanni da yan Najeriya don magance kallubalen tsaro.
Ya ce, "yana da muhimmanci shugabanni su bibiyi hanyoyin magance kallubalen tsaro.
"Ba dai-dai bane mu dumama siyasar kasar a maimakon mu hada kai wuri guda mu gano hanyar warware matsalar tsaro da tattalin arziki. Nauyi ne da ya rataya a kan mu baki daya, yan kasa da shugabanni."
Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada A Ji Ya Goyi Bayan A Tsige Buhari
A wani rahoton, Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benue ya goyi bayan yunkurin da majalisar dattawa na tsige Shugaba Muhammadu Buhari saboda matsalar tsaro da ke adabar kasar.
A cewar wani rahoto da jaridar ThisDay ta fitar, Gwamna Ortom na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya jinajinawa majalisar tarayyar kan wa'adin sati-shida da ta bawa shugaban kasa.
Gwamna Ortom ya bayyana goyon bayansan ne a masaukinsa da ke Abuja, ranar Juma'a 29 ga watan Yuli yayin tarbar tawagar yan majalisa marasa rinjaye da Sanata Philip Aduda ya yi wa jagoranci.
Asali: Legit.ng