Mambobin APC ne kan gaba wajen neman tsige Buhari, in ji Shekarau

Mambobin APC ne kan gaba wajen neman tsige Buhari, in ji Shekarau

  • Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya Ibrahim Shekarau ya ce mambobin jam'iyyar APC mai mulki ke ne kan gaba wajen neman tsige Buhari daga karagar Mulki
  • Ibrahim Shekarau ya ce yan majalisa sun gabatar da kudurin tsige shugaba Buhari da sharadin in bai dau mataki akan tabarbarewar tsaro a kasar ba za su yi waje dashi
  • Tsohon gwamnan Kano ya dai ce ba zai ambaci suna ba, amma dai mutum na farko da ya soma gabatar da kudirin tsige Buhari dan APC ne

Jihar Kano - Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Ibrahim Shekarau,yace mambobin jam’iyyar APC suka soma gabatar da yunkurin Tsige shugaba Buhari daga karagar mulkin kasar. Rahoton BBC

Sun gabatar da kudurin tsige shugaba Buhari da sharadin ya gaggauta daukar mataki akan tabarbarewar tsaro a kasar ko su yi waje dashi.

Kara karanta wannan

Sanata Daga Arewa Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Baya Goyon Bayan Tsige Buhari

Malam Ibrahim Shekarau wanda ke cikin kwamitin tsaro na majalisar dattiawan Najeriya ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa.

SHEKARAU
Mambobin APC ne kan gaba wajen neman tsige Buhari, in ji Shekarau FOTO Legit.NG
Asali: Facebook

Shekarau, ya ce an shafe sama da sa’a biyu ana cecekuce a majalisar Dattawa akan batun matsalar tsaro inda kowa ya tofa albarkacin bakin sa, har ta kai ga matsayin tura takardar neman tsige shugabankasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kudirin tsige Buhari daga mulki kan matsalar tsaro a Najeriya ya janyo tarzoma a zauren majalisa sakamakon zazzafar tattaunawa da sanatoci suka yi a tsakaninsu.

Tsohon gwamnan Kano ya dai ce ba zai ambaci suna ba, amma dai mutum na farko da ya soma gabatar da batun tsige shugabankasa a majalisa Dattawa mamba APC ne, haka zalika mutum na biyu da ya goyi bayansa kafin sauran sanatoci shima dan APC ne.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Fitaccen Sanatan APC Daga Arewa Ya Goyi Bayan A Tsige Buhari

An Baiwa Jami’in Karotan Da Ya Kama Manyan Motocin Giya, Tukuicin Naira Miliyan 1

A wani labari kuma, Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta baiwa daya daga cikin jami’anta Halilu Jalo kyautar Naira miliyan 1 bisa kama wasu manyan motoci guda biyu da giya a jihar. Rahoton Premium Times

Mista Jalo ya ki karbar cin hancin Naira 500,000 da aka ce mai barasa ya ba shi domin a sako motocin da aka kwace. Read more:

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa