2023: Babachir Lawal Ya Bayyana Yadda Kiristocin Arewa Za Su Yaki Tikitin Musulmi Da Musulmi

2023: Babachir Lawal Ya Bayyana Yadda Kiristocin Arewa Za Su Yaki Tikitin Musulmi Da Musulmi

  • Batun tsayar da musulmi biyu a matsayin dan takarar shugaban kasa da mataimaki da APC ta yi na cigaba da janyo cece-kuce
  • Babachir Lawal, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, ya ce kiristocin arewa za su yi amfani da addu'a da katin zabe don yakar abin
  • Jigon na APC ya ce akwai wata makarkashiya a jam'iyyar ta APC na yunkurin murkushe kiristocin arewacin Najeriya amma ba za su bari hakan ya faru ba kuma a shirye suke

Babachir Lawal, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, SGF, ya ce za a yaki tikitin musulmi da musulmi na jam'iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2023 da addu'a.

Lawal ya bayyana hakan ne yayin wani taro na shugabannin Kiristan Arewa da aka yi a ranar Juma'a, The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Fitaccen malami: APC faduwa za ta yi a zaben 2023 mai zuwa saboda duk musulmai ne 'yan takarar

Babachir Lawal
Babachir Lawal Ya Bayyana Yadda Kiristocin Arewa Za Su Yaki Tikitin Musulmi Da Musulmi A Zaben 2023. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC, ya zabi, Kashim Shettima, tsohon gwamnan Borno, wanda shima musulmi ne a matsayin mataimakinsa a zaben 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakan ya janyo korafi daga masu ruwa da tsaki musamman kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN.

Da ya ke tsokaci kan batun, Lawal ya ce:

"Tabbas, akwai makarkashiya ta siyasa, addini da na tattalin arziki da kuma danne kiristocin arewacin Najeriya. Amma a shirye muke.
"Za mu kare kan mu. Katin zabe na PVC da addu'a ne makaman da muka zaba kuma za mu yi amfani da su sosai a 2023."

Lawal ya ce ajandar tikitin musulmi da musulmi yanzu ma ta fara wanzuwa, ya kara da cewa kiristoci ba za su lamunci hakan ba.

Ya cigaba da cewa yin tikitin musulmi da musulmi lamari ne da aka dade ana shiryawa don haka batun cancanta yasa aka zabi mataimakin ba gaskiya bane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164