Tinubu Ya Jinjinawa Sabon shugaban Kungiyar Kristocin Najeriya CAN

Tinubu Ya Jinjinawa Sabon shugaban Kungiyar Kristocin Najeriya CAN

  • Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana Rev. Daniel Okoh zababben shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) a matsayin fitaccen shugaba wanda ya cancanta
  • A ranar Litinin Kungiyar Kiristocn Najeriya Ta zabi Rev. Daniel Okoh a matsayin sabon shugaban kungiyar
  • Tinubu ya ce sabon shugaban CAN Ya cancanci maye gurbin Rev. Ayokunle tsohon shugaban kungiyar CAN saboda kwazo da tsantseni da yake da shi

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana Rev. Daniel Okoh zababben shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) a matsayin fitaccen shugaba wanda ya cancanta. Rahoton TheNation

Asiwaju Ahemd Tinubu ya mika sakon taya murna ga Okoh, a wata sanarwa da hadimin sa kan harkokin yada labarai, Tunde Rahman ya fitar a Abuja ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa tayi Martani Mai Zafi ga Sanatocin da ke Yunkurin tsige Buhari

An zabi Rev. Okoh ne a ranar Litinin domin ya gaji Rev. Samson Olusupo Ayokunle, bayan ya kammala wa’adinsa a matsayin shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya CAN.

Tinubu
Tinubu Ya Jinjinawa Ga Sabon shugaban Kungiyar Kristocin Najeriya CAN The Nation
Asali: Facebook

Tinubu ya ce sabon shugaban CAN, wanda shi ne Babban Shugaban Cocin Christ Holy Church, ya cancanci maye gurbin Rev. Ayokunle tsohon shugaban kungiyar CAN saboda kwazo, tsantseni da hikimar sa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jagoran jam’iyyar APC ya bayyana cewa Najeriya tana tsammanin shugabanci na gari da wayewa daga Rev. Okoh.

Takarar Musulmi da Musulmi Dabarace Kawai Na Mayar Da Kirista Koma Bayan Musulmi - CAN

A wani labari kuma, Sabon shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya, Archbishop Daniel Okoh, ya ce da yawa daga cikin mabiya addinin kirista suna tsoron cewa ana kitsa makirci da gangan dan mayar da su ‘yan kasa na biyu a Najeriya.

Ya ce fargabar ta samo asali ne daga abubuwan da ke faruwa a harkokin siyasar kasar, wato tikitin tsayar da yan addini daya takara daga cikin daya daga manyan jam'iyyun siyasa a Najeriya duk da jan kune da kungiyar CAN ta yi kada ayi haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa