Yan Majalisar Wakilai sun bi sahun Sanatoci na barazanar tsige Shugaba Buhari

Yan Majalisar Wakilai sun bi sahun Sanatoci na barazanar tsige Shugaba Buhari

  • Mambobin Majalisar Wakilai bangaren marasa Rinjaye sun bai wa Shugaba Buhari Wa’adin mako shida ya kawo karshen tabarbarewar tsaro a Najeriya ko su tsige shi
  • Elemelu ya ja hankalin gwamnatin Buhari kan matsalar faduwar darajar Naira ga kudaden waje da kuma matsalolin bangaren sufurin jirgin sama
  • A ranar Laraba wasu Sanatoci daga bangaren marasa rinjaye suka bayyana ra'ayin tsige Buhari muddin bai kawo karsehen matsalar tsaro ba a cikin mako shida

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Mambobin Majalisar Wakilai bangaren marasa Rinjaye sun bai wa Shugaba Buhari Wa’adin mako shida ya kawo karshen tabarbarewar tsaro a Najeriya ko su tsige shi.

Yan majalissar wakilan sun bi sahun takwarorinsu ne na Majalisar Dattijai da suka ba shugaba Buhari wa’adin mako shida ya kawo karshen matsalar tsaro ko su tsige shi a ranar Laraba..

Kara karanta wannan

Ku kiyayi Abuja, akwai matukar hatsari a cikinta: 'Dan majalisa ya gargadi abokan aikinsa

Ndudi Elumelu, Shugaban marasa rinjaye a majalisar ya bayyana hakan bayan wata ganawa ta sirri da takwarorinsu sanatoci a jiya Alhamis.

House
Yan Majalisar Wakilai sun bi sahun Sanatoci na barazanar tsige Shugaba Buhari FOTO Legit.NG
Asali: Twitter

Elumelu ya ce muddin Buhari ya kasa kawo karshen matsalar tsaro da ake ciki a kasar, za su fara daukar matakin tsige shi daga karagar mulki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan matsalar ta tsaro, Elemulu ya kara jan hankalin gwamnatin Buhari kan matsalar faduwar darajar Naira ga kudaden waje da kuma matsalolin bangaren sufurin jirgin sama.

A ranar Laraba 27 ga Watan Yulin 2022, wasu Sanatoci daga bangaren marasa rinjaye suka fice daga zauren majalisar, a lokacin da sanata Philip Aduda ya nemi shugaban majalisar Sanata Ahmed Lawan ya ba shi damar gabatar da bukatar jawabi akan tsaro da kuma neman tsige Shugaba Buhari.

Takarar Musulmi da Musulmi Dabarace Kawai Na Mayar Da Kirista Koma Bayan Musulmi - CAN

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wasu 'yan majalisu sun shiga ganawar sirri don tattauna batun tsige Buhari

A wani labari kumaa, Sabon shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya, Archbishop Daniel Okoh, ya ce da yawa daga cikin mabiya addinin kirista suna tsoron cewa ana kitsa makirci da gangan dan mayar da su ‘yan kasa na biyu a Najeriya.

Ya ce fargabar ta samo asali ne daga abubuwan da ke faruwa a harkokin siyasar kasar, wato tikitin tsayar da yan addini daya takara daga cikin daya daga manyan jam'iyyun siyasa a Najeriya duk da jan kune da kungiyar CAN ta yi kada ayi haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa