Ka Mutunta Alƙawarin Da Ka Ɗauka, Jigon APC Ya Faɗa Wa Gwamna Wike
- Babban jigon APC a jihar Ribas ya tuna wa gwamna Nyesom Wike alƙawarin da ya ɗaukar wa yan Najeriya game da zaɓen 2023
- Chief Eze, wanda makusanci ne ga Rotimi Amaechi, ya nemi Wike ya mutunta alaƙwarin da ya ɗauka na goyon bayan kowaye
- Wannan na zuwa ne bayan Wike ya ce zai fallasa abubuwan da suka faru a PDP da kuma abinda ya shafi Atiku
Rivers - Wani jigon jam'iyyar APC a jihar Ribas, Chief Chukwuemeka Eze, ya yi kira ga gwamnan jihar, Nyesom Wike, ya mutunta alƙawarin da ya ɗaukar wa yan Najeriya yayin zaɓen fidda ɗan takarar shugaban kasa na PDP.
Eze, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya tunatar da Wike alƙwarin da ya ɗauka cewa zai goyi bayan duk wanda aka bayyana a matsayin ɗan takara a zaɓen 2023.
A sanarwan da Punch ta ruwaito, Eze ya ce Wike ya faɗa ba tare da tantanma ba cewa zai goyi baya da kuma aiki tukuru wajen ganin jam'iyyar PDP ta lashe kujerar shugaban ƙasa.
Chief Eze ya yi wannan kalamai ne kan barazanar da gwamnan ya yi na fallasa abubuwan da ke faruwa a PDP biyo bayan wata hira da ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Me gwamnan zai faɗa mana? - Eze
Jigon wanda makusanci ne ga tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce irin wannan barazanar ba abakin komai take ba, inda ya ƙara da cewa babu wani abu sabo game da PDP da Atiku Abubakar.
Leadership ta rahoto Eze ya ce:
"Shin yana kokarin faɗa mana cewa bai ɓarnatar da kuɗaɗen Ribas ba a kokarinsa na lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na PDP wanda ya sha kaye? Ko yana son faɗa mana bai shirya yadda za'a zaɓe shi ɗan takarar mataimaki ba?"
"Ko kuma Wike yana shirin faɗa mana ba shi ne ya sha alwashin goyon bayan duk wanda aka ayyana ɗan takarar PDP ba? Idan ya manta, ya kamata ya sake sauraron faifan Bidiyon da ya sha alwashin cikakken goyon bayan wanda PDP ta tsayar."
"Na shawarci Wike ya rungumi kaddara kan abin da ya wuce tun da duk shirinsa ya wargaje tun daga rashin samun tikitin shugaban ƙasa da kujerar ɗan takarar mataimaki."
A wani labarin kuma Gwamnoni uku da wasu jiga-jigan APC sun ziyar ɗan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu a Abuja
Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna da wasu gwamnonin arewa biyu sun ziyarci jagoran APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a Abuja.
Abokin takarar Tinubu, Sanata Kashin Shettima, Sakataren APC na ƙasa da tsohon shugaba, Oshiomhole sun halarci taron.
Asali: Legit.ng