Nan Ba Da Jimawa Ba Zan Fallasa Komai Game Da Atiku, Gwamna Wike
- Gwamna Wike na jihar Ribas ya ce nan ba da jimawa ba zai buɗe baki ya yi magana kan Atiku don kowa ya sani
- Tun bayan gama zaɓen fidda gwani, rikicin ya ɓarke a jam'iyyar PDP, Wike ya ce zai faɗi duk abinda ya wakana
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, ya ce bai ɗauki Wike bane saboda yana son wanda zai ji daɗin aiki da shi
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana aniyarsa na yin tsokaci kan rikicin da ya biyo bayan zaɓen fidda ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Gwamnan ya ce, na musamman zai yi magana kan ɗan takarar shugaban kasa da PDP ta tsayar, Alhaji Atiku Abubakar, domin tabbatar da yan Najeriya sun san gaskiyar abubuwan da suka faru a PDP.
A ranar 28 ga watan Mayu, 2022, Atiku ya samu nasarar lallasa Wike da sauran yan takara a babban taron PDP na musamman da ya gudana a birnin tarayya Abuja.
Gwamna Wike, wanda daga baya akai tsammanin shi zai zama abokin takarar Atiku, ya sake rasa muƙamin ga gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tun bayan abubuwna da suka faru, Gwamnan ya kama bakinsa ya yi shiru game da dambarwar da ta biyo bayan zaɓen fidda gwanin.
Sai dai gwamnan ya gana da manyan jiga-jigan jam'iyyar APC da sauran jam'iyyu, hakan ya jefa damuwa da rashin tabbas ga babbar jam'iyyar hamayya.
Da yake hira da kafar talabijin ta Arise TV, Atiku ya ce ya ƙi zaɓen gwamna Wike a matsayin abokin takararsa ne saboda yana son ya zaɓi wanda zai ji daɗin aiki da shi.
Zan yi magana kan Atiku - Wike
Da yake martani kan maganar Atiku, Gwamna Wike ya rubuta a shafinsa na Tuwita cewa yan Najeriya zasu san gaskiya da zaran ya buɗe baki ya yi magana.
"Game da Atiku, zan buɗe baki na yi magana nan ba da jimawa ba kuma yan Najeriya zasu san ainihin gaskiya kan duk wani abu da ya faru a PDP a baya-bayan nan."
A wani labarin kuma Gwamnonin jam'iyyar PDP huɗu da sike shirin ficewa daga jam'iyyar sun gana da juna, sun ɗauki mataki
Gwamna Samuel Ortom na Benuwai ya ce shi da takwarorinsa uku da suka fusata sun yanke cigaba da zama a jam'iyyar PDP.
Gwamna Wike na jihar Ribas, Gwamna Makinde na Oyo da gwamnan Abiya sun ƙauracewa harkokin PDP tun bayan abun da ya faru.
Asali: Legit.ng